Trump: Amurka Ta Lissafa Jihohin Najeriya 18 Masu Hadari, Ta Gargadi Mutanen ta
- Gwamnatin Amurka ta shawarci 'yan kasarta su sake nazari kan tafiya Najeriya saboda hare-hare da satar mutane
- Rahoton ya ce wasu sassan Najeriya na fama da rashin tsaro da rashin wadatattun cibiyoyin lafiya da magunguna
- Kasar Amurka ta ce jihohi 18 a Najeriya suna da hadari matuka ga rayuwar jama'a, ciki har da Borno, Kaduna da Rivers
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin kasar Amurka ta fitar da sabuwar shawara ga 'yan kasarta, tana bukatar su sake tunani kafin yin tafiya zuwa Najeriya.
Wannan gargadin ya zo ne saboda matsalolin rashin tsaro, ta’addanci, da karancin kayayyakin kiwon lafiya a kasar.

Source: Getty Images
Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne daga ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya, inda ta bayyana cewa dukkanin wuraren da aka lissafa a kasar suna da hadari.
Jihohin da Amurka ta yi gargadi a kai
Gwamnatin Amurka ta lissafa jihohi 18 da ta ce ya kamata a kauce musu gaba daya saboda tsananin hadari.
Jihohin da ta ambata sun hada da Borno, Yobe, Kogi da Adamawa saboda ta’addanci da satar mutane.
Sauran jihohin su ne Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara, wadanda aka ambata saboda karancin tsaro da yawaitar satar mutane da matsalar ‘yan bindiga.
Haka kuma, an gargadi 'yan kasar da kada su shiga jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo da Rivers saboda yawan fashi da makami da satar mutane a jihohin.
Amurka ta yi magana kan kiwon lafiya
Rahoton ya kara jaddada cewa ba a iya samun ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a Najeriya kamar yadda ake da su a Amurka.
Ya ce yawancin asibitocin Najeriya ba su da wadatattun kayan aiki na zamani ko kwararrun likitoci.
Haka kuma, rahoton Amurka ya ce ba a samun magunguna da dama, ciki har da na asma da ciwon sukari.

Source: Facebook
Ya bukaci matafiya su tanadi isassun magunguna kafin zuwa Najeriya, saboda cin karo da jabun magunguna ya zama ruwan dare.
Rahoton ya kuma bukaci masu shirin tafiya su sabunta rigakafin cututtuka kamar su cutar shawara, kyanda, cutar sankarau kafin zuwan su Najeriya.
Yaduwar ta’addanci da hare-hare a jihohi
Rahoton ya bayyana cewa ‘yan ta’adda suna ci gaba da kulla makirci da kai farmaki a sassa daban-daban na Najeriya.
Baya ga Najeriya, kasar Amurka ta hada wasu kasashen Afirka 11 cikin jerin wadanda take gargadin tafiya zuwa cikinsu.
Rahoton Business Insider Africa ya ce kasashen sun hada da Somaliya, Libiya, Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Bayanan tsaro daga Amurka a baya
Ba sabon abu ba ne a tarihin diflomasiyyar Amurka ta rika fitar da gargadi ga 'yan ƙasarta game da yin tafiya zuwa Najeriya.
A duk shekara ko bayan wani lokaci, gwamnatin Amurka ta hannun ofishinta na jakadanci a Abuja kan sabunta irin wannan shawara, musamman idan akwai hauhawar rashin tsaro ko barkewar cututtuka.
Tun bayan ƙarfafa ayyukan 'yan ta’adda a Arewa maso Gabas da kuma yawaitar satar mutane a wasu sassan ƙasar, Amurka ta fi bayyana damuwarta da irin hadurran da matafiya za su iya fuskanta.
Wannan ya sa sau da dama ta lissafa wasu jihohi a matsayin wuraren da bai dace a ziyarta ba, ciki har da Borno, Yobe, Zamfara, da Rivers.
Haka kuma, Amurka na yawan caccakar tsarin lafiya na Najeriya, tana jaddada cewa yawancin asibitoci ba su da ingantaccen kayan aiki, kuma akwai ƙarancin magunguna da kwararrun likitoci.
Irin wannan gargadi ya saba fitowa, musamman kafin manyan bukukuwa, lokacin zabe, ko lokacin da ake samun hauhawar tashe-tashen hankula.
Wannan ya nuna cewa Amurka na ci gaba da daukar matakin kariya ga 'yan ƙasarta a duk inda suke.
Amurka na son turo 'yan cirani Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya ce shugaban Amurka na son turo 'yan cirani Afirka.
Yusuf Tuggar ya ce shugaba Donald Trump yana son Najeriya ta karbi wasu daga cikin 'yan ciranin.
Duk da haka, ministan ya ce Najeriya ba za ta yarda da bukatar Trump ba saboda ita ma tana da tarin matsalolin cikin gida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


