Dubu Ta Cika: Rikakken Dillalin Kwayoyi Ya Shiga Hannu bayan Shekara 6 Ana Nemansa
- Jami'an hukumar NDLEA ta kama Okpara Paul Chigozie, shugaban dillalan kwayoyi da ake nema ruwa a jallo tun 2019, a jihar Legas
- An gano kilo 7.6 na hodar iblis da giram 900 na methamphetamine a cikin motarsa, yayin da aka gano karin kwayoyi a gidansa
- A wani samame daban, NDLEA tare da FAAN sun kwato kwayoyin tramadol da Rohypnol guda 7,790 a hannun wani fasinjan Italiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar NDLEA ta kama wani fitaccen shugaban masu safarar kwayoyi mai suna Okpara Paul Chigozie mai shekaru 60, wanda ya shafe shekaru shida yana guje wa hukuma.
An cafke wanda ake zargin ne a maboyarsa yayin da yake ƙoƙarin jigilar miyagun kwayoyi iri-iri zuwa yankin Kudu maso Gabas da wasu sassan Najeriya.

Source: Twitter
NDLEA ta kama shugaban dillallan kwayoyi
Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin NDLEA na X a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama Okpara Chigozie, wanda ke cikin jerin mutanen da NDLEA ke nema tun shekarar 2019 a ɓoyayyen wurinsa da ke yankin Isheri a Legas a ranar 13 ga Yuli.
Babafemi ya ce hakan ya biyo bayan tare wasu daga cikin kayansa da aka yi da misalin ƙarfe 5:45 na safiya a Ilasamaja, kan babbar hanyar Apapa-Oshodi.
A cewarsa, tawagar jami'an NDLEA, bisa ga bayanan sirri da suka samu, sun kama ɗaya daga cikin direbobin da ke jigilar kayan babban dillalin kwayoyin a kan hanyarsa ta zuwa Onitsha, Anambra, a cikin wata farar motar Toyota Sienna.
An gono hodar iblis da methamphetamine
Babafemi ya ƙara da cewa jami’an NDLEA sun yi amfani da karnukan gano kwayoyi don binciken motar, kuma a ciki suka gano 7.6kg na hodar iblis da 900g na metham-phetamine da aka ɓoye a sassan motar.
"An kawo karnukan bincike na hukumar nan da nan don su bincika motar bayan an samu kilo 7.6 na hodar iblis da gram 900 na metham-phetamine a ɓoye a cikin sassan jikin motar.
“A ci gaba da samamen, jami’an NDLEA sun afka maboyar Okpara da ke Isheri, inda aka ƙara gano kilo 1.8 na hodar iblis da kilo 1.3 na metham-phetamine."
- Femi Babafemi.

Source: Getty Images
An kama tramadol da Rohypnol guda 7,790
Babafemi ya kuma ce jami'an NDLEA, a wani aiki na haɗin gwiwa tare da jami'an tsaron jirgin sama na hukumar FAAN, sun kwato kwayoyin tramadol da Rohypnol guda 7,790.
Babafemi ya ce an tare miyagun kwayoyin, waɗanda ke cikin kayan wani fasinja da ke hanyar zuwa Italiya, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed a ranar Laraba.
Ya ce wanda ake zargin, wanda ke zuwa Italiya ta Istanbul a jirgin Turkish Airlines, ya yi ikirarin cewa ya sayi magungunan da kansa, yana fatan sayar da su a wancan ƙasar a farashi mafi tsada.
Fusatattu sun bankawa jami'in NDLEA wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fusatattun mutane sun bankawa jami'in NDLEA, Aliyu Imran wuta a Gadan-Gayan, Kaduna, bayan wani hatsari da ya yi ajalin mutum uku.
Bayan hatsarin ya afku, an ce Imran ne ya tsaya ya na kokarin kwantar da tarzoma, amma fusatattun suka soka masa wuka tare da banka masa wuta har lahira.
Iyalansa sun zargi NDLEA da rashin daukar mataki ko yi masu jaje, amma hukumar ta musanta, tana mai cewa ta tura tawaga don jajantawa iyalan.
Asali: Legit.ng


