"Ta Ɗauki Wuka, Ni Na Ɗauki Guduma": Saurayi Ya Faɗi Yadda Ya Kashe Budurwarsa
- Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta cafke wani matashi, Ubakpororo Kelvin, wanda ake zargin ya kashe budurwarsa mai yara biyu
- SP Bright Edafe ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin maye lokacin da ya bagawa budurwar guduma sau uku har ta mutu
- Ubakpororo ya bayyana cewa ya sha tramadol da wata kwayar kafin kisan kuma yana nadamar kashe mahaifiyar ‘ya’yansa biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - Wani matashi ɗan shekara 27, Ubakpororo Kelvin, wanda ya gudu bayan da ake zargin ya kashe budurwarsa, ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan Delta.
Rahotanni sun bayyana cewa Ubakpororo ya kashe budurwarsa kuma uwa ga ‘ya’yansa biyu, mai suna Excel Ukeredi Peace, a ranar 26 ga Yuni, 2025, sannan ya tsere.

Source: Twitter
An kama matashi kan kashe budurwarsa
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SP Bright Edafe ya ce:
“Za ku tuna cewa tsakanin ranakun 26 da 27 ga Yuni, 2025, kafafen sada zumunta suka cika da labarin kisan gillar da aka yi wa wata budurwa mai suna Excellence a Sapele, kisan da ake zargin saurayinta kuma mahaifin ‘ya’yanta biyu ya aikata.
“Da farko wanda ake zargin ya gudu, amma daga baya mun kama shi, kuma yanzu yana hannun rundunar 'yan sanda.
“Ga dukkan masu neman adalci ga marigayiya Excellence, muna sanar da ku cewa an kama wanda ake zargi, kuma za a gurfanar da shi a kotu nan ba da jimawa ba.”
Matashi ya kashe budurwarsa da guduma
Da yake amsa laifinsa, wanda ake zargi Ubakpororo ya ce yana cikin maye ne lokacin da ya aikata kisan.
“Budurwata tana harkar lalata da maza. Duk lokacin da ta zo gidana, sai ta canza kaya ta fita ta tafi wajen wani namiji.
“Ranar da abin ya faru, mun yi samu sabani da ita a gidana. Mun yi cacar baki sosai. Ta ɗauki wuka, ni kuma na ɗauki guduma.
“Bayan na rinjaye ta, na buge ta da guduma sau uku a goshi, sannan ta faɗi ta mutu. Da na fahimci ta mutu, na yi ƙoƙarin faɗowa daga bene domin in mutu tare da ita, amma hakan ya ci tura."

Source: Twitter
"Ina cikin maye na yi kisan" - Matashi
Matashin ya shaidawa 'yan sanda cewa:
“Lokacin da na bug mata guduma, ban yi zaton za ta mutu ba. Kuskure ne. Ina matuƙar bakin ciki. Ta haifa mini ‘ya’ya biyu — ɗaya shekara uku, ɗaya shekara biyu. Ban cikin hayyacina lokacin.
“Ranar na sha tramadol har miligram 100 sannan na sha kwayar ‘loud’. Tasirin wadannan kwayoyi ne ya sa na aikata haka. Ban jima da fara shan wadannan kwayoyin ba.”
Wanda ake zargin ya kuma amsa cewa yana harkar damfara ta yanar gizo (wanda ake kira ‘yahoo’), sannan ya bayyana nadamarsa kan kashe mahaifiyar ‘ya’yansa.
Kalli bidiyon sanarwar a nan kasa:
Saurayi ya kashe budurwarsa bayan lalata
A wani labarin, mun ruwaito cewa, matashi mai shekara 19 Muhammad Ibrahim ya kashe budurwarsa saboda ta nemi ya biya N5,000 bayan sun gama lalata.
Hatsaniya kan biyan kudin ta kaure tsakanin masoyan har ta kai ga doki in doke ka, abin ya zo da karar kwana Ibrahim ya daba wa budurwar wuka.
Duk da kokarin jama'a na ceton budurwar, rai ya yi halinsa, inda shi ma Ibrahim ya gamu da fushin mutane, amma 'yan sanda suka cece shi.
Asali: Legit.ng

