Wata sabuwa: Saurayi ɗan shekaru 12 ya kashe budurwar sa mai shekaru 15 a Jigawa

Wata sabuwa: Saurayi ɗan shekaru 12 ya kashe budurwar sa mai shekaru 15 a Jigawa

- Saurayi dan shekaru 12 ya harbe budurwarsa har lahira a wani kauyen Jigawa

- Lamarin ya afku ne a ranar Asabar da rana lokacin da budurwar ke wasa a gidan kawunta

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin inda tace ana kan bincike

Wani matashi dan shekaru 12 mai suna Muhammadu Sani ya kashe budurwarsa mai shekaru 15 a kauyen Damutawa da ke karamar hukumar Jahun ta jihar Jigawa.

An yi zargin cewa Muhammadu ya halaka budurwar tasa mai suna Habiba Junaid a ranar Asabar da misalin karfe 2:00 na rana lokacin da take wasa a wajen kawunta, PMNews ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga: Ƙungiyar Arewa ta juyawa Gumi baya, ta ce ya je ya ƙwaci kansa

Wata sabuwa: Saurayi ɗan shekaru 12 ya kashe budurwar sa mai shekaru 15 a Jigawa
Wata sabuwa: Saurayi ɗan shekaru 12 ya kashe budurwar sa mai shekaru 15 a Jigawa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Muhammadu ya dauki bindigar kawun nata sannan ya harbi Habiba a baya. A nan take ta mutu.

Kakakin yan sandan jihar Jigawa, ASP Zubairu Aminudeen Ismail ya tabbatar da lamarin inda ya ce bayan yan sanda sun samu labarin, sun yi gaggawan daukar ta zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

Kakakin yan sandan ya ce an kwato bindigar sannan aka kama wanda ake zargin yayinda har yanzu ake ci gaba da bincike.

KU KARANTA KUMA: Kagara: Dogo-Gide, shugaban 'yan bindiga ya tuntubi iyayen yara a kan kudin fansa

A wani labari, wata mata mai shekaru 91 a duniya ta auri sahibinta, wani mutum mai shekaru 73 bayan shafe shekaru fiye da 10 suna soyayya, rahoton jaridar The Nation. An kuma gwangwaje biki na kece raini a ranar daurin auren na su.

Matar mai suna Evelina Meadder ta auri saurayinta da suka dade tare mai suna Calgent Wilson mai shekaru 73 a wani babban biki da aka shirya a kasar Jamaica.

A cewar rahoton da The Mirror ta wallafa, ma'auratan sun fara soyayya ne tun a shekarar 2009 a lokacin da Evelina ta kamu da rashin lafiya, shi kuma Calgent, manomi, ya yi jinyarta har zuwa lokacin da ta warke.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel