Kogi: Malamin Jami'a Ya Mutu Yana Tsakiyar Lalata da Ɗalibarsa, An ga Gawarsa a Otal

Kogi: Malamin Jami'a Ya Mutu Yana Tsakiyar Lalata da Ɗalibarsa, An ga Gawarsa a Otal

  • Dr. Olabode Ibikunle, babban malami a Jami’ar PAAU da ke Kogi, ya rasu yayin da yake lalata da wata ɗaliba a wani otal a Anyigba
  • Rundunar ’yan sandan Kogi ta ce an gudanar da binciken gawa, kuma an kama ɗalibar da suka yi lalata tare malamin don ƙarin bincike
  • Rahotanni sun nuna cewa malamin, wanda ke da mata da ƴaƴa, ya sha magungunan ƙara kuzari kafin ya mutu yana jima'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Wani babban malami a Jami’ar Prince Abubakar Audu (PAAU) da ke Anyigba, jihar Kogi, Dr. Olabode Abimbola Ibikunle, ya rasu yana tsakiyar lalata da wata ɗaliba.

Lamarin ya faru ne a wani otal da ke garin Anyigba a ranar Talata, 15 ga Yulin, 2025, kuma manajan otal ɗin ne ya kai rahoto ga ’yan sanda.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Zamfara, an samu asarar rayuka

'Yan sana sun fitar da rahoto kan malamin jami'ar PAAU da ya mutu yana lalata da dalibarsa a Kogi
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kogi: Malami ya mutu yana lalata da daliba

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Juma’a a Lokoja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SP Aya ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa an riga an gudanar da binciken gawar malamin domin gano musabbabin rasuwarsa.

A cewarsa, manajan otal ɗin, Moses Friday, ya bayar da rahoton cewa wata ɗaliba ’yar aji biyu, Gloria Samuel, mai shekara 22 ta ruga zuwa wajen karɓar baƙi na otal ɗin tana neman taimako, inda ta malamin ya yanke jiki ya faɗi suna cikin lalatarsu.

’Yan sanda suka isa wajen cikin gaggawa, aka garzaya da malamin asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

An kama dalibar da ta yi lalata da malamin

Rundunar ’yan sanda ta ce bincike na ci gaba da gudana kuma za a ɗauki mataki bisa abinda binciken ya nuna.

Kara karanta wannan

Atiku ya buɗe kofa, Sanata na 2 ya fice daga jam'iyyar PDP a ƙasa da awanni 24

Wani ɗalibi da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa malamin yana jima’i da ɗalibar kafin ya yanke jiki ya rasu, inji rahoton Vanguard.

An kama ɗalibar aka kai ta ofishin ’yan sanda, daga bisani aka mayar da ita zuwa Sashen Binciken Laifuffuka na Jiha (SCID) domin ƙarin bincike.

Ibikunle, wanda ake cewa yana da mata da yara, an ce ya shiga otal ɗin tun da safe tare da ɗalibar da ke karatu a sashen koyar da darasin zamantakewa.

Ana zargin malamin jami'ar Kogi ya sha maganin karin karfin maza ya mutu yana lalata da daliba
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kogi a Arewa maso Gabashin kasar. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An dakatar da malami kan zargin lalata

Rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce malamin ya sha magungunan ƙara kuzari masu yawa kafin faruwar lamarin.

Ba wannan ne karon farko da aka samu malamin jami'a yana lalata da dalibai mata ba, ko a Afrilun 2024, sai da Jami'ar Najeriya, Nsukka (NU) ta dakatar da wani malami kan zargin lalata da daliba.

A wancan lokacin, mun ruwaito cewa an kama malamin ne a bidiyo yana lalata da dalibar, wanda ya sa jami'ar ta dakatar da malamin har sai ta yi bincike.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, Bola Tinubu zai je jihar Kano ta'aziyyar Aminu Dantata

Dan sanda ya mutu yana lalata da budurwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Lawal Ibrahim, wani jami'in dan sanda daga sashen rundunar na Kwali, ya mutu a wani otel da ke Gwagwalada.

An gano cewa Lawal ya haɗu da Maryam Abba a shafukan sada zumunta watanni uku da suka gabata, inda suka yi sharholiya a otel din.

Tuni dai aka ce hukuma ta kama Maryam yayin da 'yan sandan suka ki cewa komai game da jami'insu da ya mutu a wannan yanayi .

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com