Tirkashi: Jami'an NSCDC, NIS Sun Yi Garkuwa da Ɗan Uwansu, Sun Karɓi N30m Kuɗin Fansa

Tirkashi: Jami'an NSCDC, NIS Sun Yi Garkuwa da Ɗan Uwansu, Sun Karɓi N30m Kuɗin Fansa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta kama Juliet da Ngozi Chukwu, ‘yan uwa mata daga Ebonyi, bisa zargin su sace dan uwansu
  • An rahoto cewa Juliet na aiki da NSCDC, sannan Ngozi na aiki a NIS, kuma sun kitsa sace babban yayansu Friday Chukwu a Ituku-Ozalla
  • 'Yan sanda sun cafke matan ne a wani dakin otel yayin da suke kasafta wani kaso daga cikin N30m da suka karba na kudin fansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu ta kama wasu ‘yan uwa mata biyu, Juliet Chukwu da Ngozi Nancy Chukwu, bisa zargin garkuwa da mutane.

Ana zargin Juliet Chukwu da Ngozi Nancy Chukwu sun kitsa sace ɗan uwansu na jini, Mista Friday Chukwu tare da karbar kudin fansa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukar matasa marasa aiki a Najeriya

'Yan sanda sun kama wasu mata 'yan gida daya da suka shirya sace dan uwansu
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan gida 1 mata sun sace dan uwansu

Rahoton Punch ya nuna cewa Juliet da Ngozi, waɗanda ‘yan asalin kauyen Amaeze ne a ƙaramar hukumar Ivo ta jihar Ebonyi, sun sace Mista Friday a watan da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Juliet Chukwu dai jami’a ce a hukumar NSCDC, yayin da Nancy Chukwu ke aiki da hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS).

A cewar rahoton, an sace Mista Chukwu ne a kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal, kusa da asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya da ke Ituku-Ozalla, a ƙaramar hukumar Nkanu ta Yamma, jihar Enugu.

Rahotanni sun ce sai da aka biya Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa kafin aka sako Mista Friday Chukwu.

Yadda aka kama wadanda ake zargin

Ana kuma zargin su Juliet da Ngozi da hannu a sace Mista Dennis Igwe, manajan kamfanin China Oriental Mining da ke a yankin, a farkon wannan mako.

Kara karanta wannan

APC ta lallasa PDP, LP, Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 20 da Kansiloli 375 a Legas

An kama su ne a wani otal yayin da suke ƙoƙarin raba kuɗin fansar da aka biya, wanda ya kai ga Naira miliyan 10.

Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Chika Nwoba, wanda ya wallafa bayanan lamarin a yanar gizo, ya zargi ‘yan uwan da yuwuwar sa hannu a sauran ayyukan laifi a yankin Ishiagu.

Ya ce suna haɗa kai da miyagu wuraren da ake shirya garkuwa da mutane, satar kayayyakin layin dogo da kuma lalata bututun mai a yankin.

Shugaban karamar hukumar Ivo a jihar Enugu ya tabbatar da kama matan da suka sace dan uwansu
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Enugu da ke kudancin kasar. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban ƙaramar hukumar Ivo, Cif Emmanuel Ajah, ya tabbatar da kama su, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce ko da yake lamarin bai faru a ƙaramar hukumar sa ba, ya riga ya tuntuɓi rundunar ‘yan sanda ta Enugu da kuma hukumar NSCDC ta jihar Ebonyi.

"Eh, mun san da lamarin. Amma ba a yankina ya faru ba. ‘Yan uwan Mista Friday Chukwu, wanda abokina ne, an kama su. Sun ce mutum shida ne ke da hannu, har yanzu ana neman mutane hudu da suka tsere.”

Kara karanta wannan

Harin ƴan bindiga: Mutane sun ji azaba, sun fara tserewa daga gidajensu a Filato

- Cif Emmanuel Ajah.

Shugaban karamar hukumar ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙari don tabbatar da tsaron al’ummar Ivo da kewaye.

Matashi ya yi garkuwa da kaninsa a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sandan jihar Kano sun kama wani matashi da ake zargi da jagorantar sace ɗan kanwar mahaifiyarsa domin karɓar kuɗin fansa.

Hisbullah Salisu ne ya shirya sace Muhammad Nasir Jamilu mai shekaru hudu daga gidansu da ke Sharada, inda aka nemi a biya kuɗin fansa Naira miliyan 10.

Rahotanni sun ce iyalan yaron sun riga sun bai wa masu garkuwar N300,000 kafin rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar cafke wanda ake zargi da laifin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com