'Ku Shirya': Yobe, Kano da Jihohi 9 Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa daga ranar Lahadi
- Ma’aikatar muhalli ta tarayya ta lissafa jihohi 11 da ta ce za su iya fuskantar ambaliyar ruwa daga 16 zuwa 20 ga Yulin 2025
- Jihohin da ake hasashen za su fuskanci ambaliya sun haɗa da Adamawa, Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Plateau da wasu shida
- Wannan na zuwa ne yayin da gwamnati ta kaddamar da shirin inshorar ambaliya domin rage asarar da ake yi sanadin ambaliya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ma’aikatar muhalli ta tarayya ta fitar da gargadi na yiwuwar ambaliya a wasu jihohi 11 tsakanin ranakun 16 da 20 ga Yuli.
Usman Bokani, darakta a cibiyar hasashen ambaliya ta kasa (NFEWC) karkashin ma’aikatar muhalli, shi ne ya fitar da sanarwar a ranar Laraba.

Source: Getty Images
Jihohi 11 da ambaliya za ta iya shafa
A cewar sanarwar, wadda jaridar The Cable ta gani, jihohi da yankunan da ake sa ran ambaliya za ta shafa sun hada da:

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Adamawa (Mubi)
- Akwa Ibom (Edor, Upenekang, Oron, Eket)
- Borno (Ngala, Maiduguri)
- Bauchi (Azare, Bauchi, Itas, Jama’are, Kafin-Madaki, Jama’a, Kari, Misau)
- Cross River (Calabar, Akpap)
- Jigawa (Miga, Gwaram, Diginsa, Ringim, Dutse)
- Katsina (Daura)
- Kano (Kunchi, Kano, Gezawa, Wudil, Bebeji, Sumaila, Tudun Wada)
- Plateau (Jos, Bukuru, Mangu)
- Yobe (Jakusko, Machina, Dapchi)
- Zamfara (Bungudu, Gusau)
Gargadin ambaliya da illarta ga Najeriya
Usman Bokani ya bukaci gwamnatocin jihohi da hukumomin da abin ya shafa su ɗauki matakan gaggawa don rage illar ambaliya ga rayuka da dukiyoyi.
Mun ruwaito cewa, hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIHSA) ta bayyana cewa jihohi 30 da babban birnin tarayya (FCT) na cikin haɗarin ambaliya a shekarar 2025.
Hukumar ta kara da cewa ana hasashen cewa garuruwa 2,187 a cikin kananan hukumomi 293 na iya fuskantar matsakaicin haɗarin ambaliya.
A shekarar 2024, ambaliya ta yi sanadin mutuwar mutane 321, ta shafi fiye da mutane miliyan 1.37, kuma ta raba sama da 740,000 da muhallansu a fadin Najeriya.

Source: Twitter
Shirin inshorar ambaliya a Najeriya
A baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta kafa shirin Inshorar Ambaliya ta Kasa a matsayin matakin rigakafi don tinkarar karuwar barazanar ambaliya a Najeriya.
An gudanar da taron kwamitin fasaha a kan tsarin aiwatar da inshorar a Abuja cikin watan Yuni, a cewar rahoton Punch.
A lokacin taron, babban sakataren ma’aikatar muhalli ta tarayya, Mahmud Kambari, ya bayyana karuwar ambaliya a sassan kasar a matsayin lamarin da ke bukatar daukin gaggawa.
Ya ce akwai bukatar a sauya salo daga mayar da martani bayan afkuwar ambaliya zuwa matakan rigakafi masu dorewa, kuma shirin inshorar na da matukar mahimmanci wajen gina ɗorewar kariya a dogon lokaci.
Kambari ya danganta yawan aukuwar ambaliya a Najeriya da sauyin yanayi, yawaitar gine-gine ba bisa tsari ba da kuma rashin wadatattun ababen more rayuwa.
Mafita kan ambaliya daga manyan Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar ACF ta ja hankalin gwamnatoci kan muhimmancin ɗaukar matakan kariya kafin aukuwar ambaliya a daminar bana.
Shugabannin Arewa sun roƙi gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi da su tanadi ingantattun hanyoyi don rage illar ambaliya ga al’umma.
ACF ta kuma bukaci jama’ar da ke zaune a yankunan da ambaliya ka iya shafa da su kare gidajensu, tare da gujewa toshe hanyoyin ruwan da ke kauyuka da birane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

