Najeriya Ta Yi Martani ga Turkiyya kan Zargin Bullar Sabuwar Kungiyar Yan Ta'addan FETO

Najeriya Ta Yi Martani ga Turkiyya kan Zargin Bullar Sabuwar Kungiyar Yan Ta'addan FETO

  • Rundunar tsaro ta ƙaryata zargin jakadan Turkiyya cewa akwai ƙungiyar ta’addanci daga kasarsa da ke aiki a Najeriya
  • Ta ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken 'yanci wacce ba za ta karɓi zargin ƙasashen waje ba idan babu sahihin bincike
  • Rundunar soji ta gargadi ‘yan Najeriya kan yawaitar farfaganda da labaran da za su iya daga hankalin jama'a kan rashin tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaRundunar tsaron Najeriya (DHQ) ta ƙaryata zargin ɓullar sabuwar kungiya ta’addanci daga Turkiyya da aka ce tana aiki a cikin ƙasar nan.

Wannan zargi ya fito ne daga bakin jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, wanda ya bayyana hakan a bikin ranar dimokuraɗiyya da haɗin kan Ƙasarsa.

Kara karanta wannan

Ficewa daga PDP: Lokuta 5 da Atiku ya sauya jam'iyya da dalilinsa

Bola Tinubu na Najeriya da Shugaban Turkiyya
Najeriya ta yi martani ga Turkiyya kan FETO Hoton: Bayo Onanuga/Getty
Source: Facebook

The Nation ta wallafa cewa jakadan ya yi iƙirarin cewa wasu ƴan ƙungiyar Fethullah (FETO) suna aiki a Najeriya karkashin cibiyoyin ilimi da na lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jakadan ya bayyana damuwa matuƙa a kan batun, inda ya ce hakan babbar barazana ne ga kowace ƙasa da suka shiga.

Martanin Najeriya ga Turkiyya

The Guardian ta ruwaito daraktan hulɗa da manema labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya musanta iƙirarin gwamnatin Turkiyya.

Ya ce babu wani bayani daga hukumominta da ke nuna cewa akwai irin wannan ƙungiya a Najeriya.

Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 17 ga Yuli, 2025.

Ya ce:

“A matsayinmu na rundunar tsaro, ba mu ɗauki wannan bayani daga jakadan Turkiyya a matsayin wani sahihin bayani ba. Kowa na da ’yancin faɗin albarkacin bakinsa, amma wannan ba yana nufin mu rungumi duk wani zargi da aka yi a kan kasarmu ba."

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan FETO sun shigo Najeriya,' Turkiyya ta gargadi Tinubu

DHQ: 'Da alaƙa tsakanin Najeriya da ƙasashen waje'

Ya ce Najeriya tana da kyakkyawar alaƙa da ƙasashen duniya ta fuskar diflomasiyya da na soji.

Rundunar sojin Najeriya ta musanya zargin Turkiyya
Najeriya ta musanya ɓullar kungiyar FETO daga Turkiyya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Manjo Janar Markus Kangye ya ce amma hakan ba yana nufin za ta bar wasu ƙasashe su riƙa shigo da ra’ayoyinsu cikin harkokinta na cikin gida ba.

Kangye ya ce:

"Ba za mu ɗauki zargin da wasu ƙasashe ke yi game da Najeriya a matsayin gaskiya ba sai mun yi nazari da bincikenmu na cikin gida. Najeriya ta san kanta, kuma rundunar sojin Najeriya na da dokoki da ƙa'idojin aiki da take bi.”

Ya kuma gargadi ’yan Najeriya da su kasance masu lura da yawaitar farfaganda da yaɗa labaran ƙarya a wasu ƙasashe da ƙungiyoyi na duniya.

Turkiyya ta gargadi Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Turkiyya ta bayyana damuwarta kan yadda ake ci gaba da ayyukan ƙungiyar FETO da ta ayyana da ƴar ta'adda a Najeriya.

Jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ne ya fadi hakan a liyafar da ofishin jakadancin ƙasar ya shirya a Abuja domin tunawa da yunƙurin juyin mulki a ƙasarsa.

Jakadan ya ƙara da cewa duk da nasarar da Turkiyya ta samu wajen dakile juyin mulkin da haɗin kan jama’a da rundunonin tsaro, har yanzu akwai barazana daga FETO a gida da waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng