Gwamnatin Tarayya Ta Saka Sabuwar Ranar Bude Shafin Daukar Ma'aikata 30,000

Gwamnatin Tarayya Ta Saka Sabuwar Ranar Bude Shafin Daukar Ma'aikata 30,000

  • Hukumar CDCFIB ta dakatar da shafinta na daukar ma’aikata saboda tangarda da matsalolin fasaha
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025 aka sanya domin sake bude shafin a fadin kasa
  • Hukumar ta bayyana dalilin dakatar da daukar aikin a matsayin son tabbatar da tsarin daukar aiki na gaskiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar dake kula da daukar ma’aikata a hukumomin tsaron cikin gida ta rufe shafin neman aiki ta yanar gizo da ta bude saboda tangarda da cunkoso na masu shiga shafin.

Hukumar ta sanar da cewa za a sake bude shafin ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025, domin bai wa matasa damar kammala cike-ciken neman aiki cikin sauki da kwanciyar hankali.

Za a bude shafin daukar ma'aikata ranar Litinin mai zuwa
Za a bude shafin daukar ma'aikata ranar Litinin mai zuwa. Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta wallafa cewa hukumar CDCFIB ta ce hakan na cikin kokarinta na tabbatar da tsari mai kyau wajen daukar ma'aikata.

Kara karanta wannan

Zambar N2.2bn: Babbar kotu ta kawo karshen shari'ar tsohon gwamnan Ekiti da EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a ranar Litinin, 14 ga Yuli ne hukumar ta bude shafin, inda ake bukatar matasa masu neman aiki su tura bayanan su.

Hukumomin da za a nemi aiki a cikinsu sun hada da hukumar shige da fice NIS, hukumar kashe gobara, hukumar gidajen gyaran hali da hukumar NSCDC.

Dalilin dakatar da daukar ma'aikata

A wata sanarwa da sakataren hukumar, Malam AM Jubril, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa an dakatar da shafin ne domin a samu damar gyara tsarin sakamakon yawan masu shiga.

The Cable ta rahoto ya ce:

“Wannan mataki zai bai wa shafin damar karbar yawan wadanda ke bukatar nema aikin ba tare da tangarda ba, tare da tabbatar da tsari na gaskiya da adalci wajen daukar ma’aikata.”

Ya kara da cewa suna jin dadin yadda matasan Najeriya ke nuna kwadayin yin hidima ga ƙasa a irin wadannan hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

An rufe majalisar Najeriya kirif saboda mutuwar shugaba Buhari

Matsalolin da aka fuskanta a shafin

Dakatarwar da aka yi ta biyo bayan korafe-korafe da dama daga matasa masu shiga shafin, wadanda suka rika fuskantar matsaloli kamar rashin iya shiga da gazawar ajiye bayanai.

Wannan dai shi ne karo na uku da hukumar ke dakatar da shirin, inda a baya ta sha alwashin gyara tsarin domin saukaka amfani da shi ga masu neman aiki.

Hukumar ta yi alkawarin cewa tana ci gaba da gyara shafin don tabbatar da cewa masu neman aiki ba za su kara fuskantar matsaloli ba.

Wasu jami'an NSCDC suna fareti a wani taro
Wasu jami'an NSCDC suna fareti a wani taro. Hoto: NSCDC Nigeria
Source: Twitter

Yaushe za a cigaba da tura bayanai?

Hukumar ta bukaci matasa da su ci gaba da bibiyar shafinta domin samun bayanai kuma su yi shiri don sake shiga shafin neman aikin daga ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025.

Ta kuma jaddada cewa hukumar za ta tabbatar da cewa dukkan masu neman aiki sun samu daidaito da adalci, ba tare da son kai ba ko wariya.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: Amurka ta rufe ofishinta a Abuja, Saudiya ta aiko da sako Najeriya

Dangote zai dauki matasa aiki

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya kara ba matasan Najeriya damar aiki da kamfanin shi.

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa za a dauki matasan ne domin ba su dama su samu horo na musamman na wucin gadi.

Sai dai ba dukkan matasan Najeriya ne za su samu damar ba, domin an kafa sharadin cewa sai wadanda suka kammala karatu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng