'Yan Ta'addan FETO Sun Shigo Najeriya,' Turkiyya Ta Gargadi Tinubu

'Yan Ta'addan FETO Sun Shigo Najeriya,' Turkiyya Ta Gargadi Tinubu

  • Gwamnatin Turkiyya ta bayyana damuwa kan cigaban ayyukan ƙungiyar FETO a Najeriya musamman a fannoni kamar ilimi da lafiya
  • Jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ya ce FETO na barazana ga kowace ƙasar da ta ke gudanar da ayyuka a cikinta
  • An bayyana cewa Turkiyya ta kwace wasu cibiyoyin da ke da alaƙa da FETO a ƙasashe daban-daban, ciki har da na ilimi da jinƙai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Turkiyya ta sake bayyana damuwarta kan ayyukan ƙungiyar da ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci, wato FETO, a Najeriya.

Jakadan kasar a Najeriya, Mehmet Poroy, ne ya bayyana hakan yayin liyafar da ofishin jakadancin Turkiyya ya shirya a Abuja domin tunawa da ranar dimokiraɗiyyarsu.

Shugaban kasar Turkiyya, Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiyya, Tayyip Erdogan. Hoto: Getty Images|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Mehmet Poroy ya yi ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Bai so": Buba Galadima ya fadi dalilin jawo Buhari cikin harkar siyasa

Bikin ya tuna da yunƙurin juyin mulki da ya faru a Turkiyya a ranar 15 ga Yuli, 2016, wanda gwamnatin ƙasar ke zargin ƙungiyar FETO da shirya shi.

'FETO na cigaba da zama barazana,' Turkiyya

Jakadan ya ce duk da cewa an ci galaba kan juyin mulkin saboda haɗin kan jama’a da dakarun tsaro, har yanzu FETO na ci gaba da zama barazana a Turkiyya da sauran ƙasashe.

A cewarsa:

“Ana ci gaba da kama mambobin ƙungiyar a Turkiyya. Ayyukan irin na wannan ƙungiya barazana ne ga kowace ƙasa da suke ciki.”

The Nation ta rahoto Poroy ya ƙara da cewa:

“Abin takaici, ƙungiyar FETO har yanzu na ci gaba da ayyukanta a Najeriya, musamman a fannoni kamar ilimi da kiwon lafiya.
“Muna sanar da abokanmu ’yan Najeriya a kai a kai game da haɗarin da ke tattare da ƙungiyar nan, tare da jan hankalinsu da su kasance masu sa ido da lura.”

Kara karanta wannan

2027: Shugaban ADC ya fallasa shirin dakile farin jinin jam'iyyar

Turkiyya na cigaba da yakar FETO a duniya

Jakadan ya bayyana cewa gwamnati a Turkiyya tare da haɗin gwiwar ƙasashe masu alaƙa da ita, sun riga sun rushe wasu cibiyoyin da ke da alaƙa da FETO a sassa daban-daban na duniya.

Ya ce an riga an karbi wasu makarantun da ke karkashin ikon ƙungiyar a baya da sunan gwamnatin Turkiyya.

Sai dai ya yi gargaɗi da cewa FETO na ci gaba da amfani da shafukan agaji da ƙungiyoyin addini don ɓoye ainihin manufarta ta shiga cikin manyan hukumomi da tsarin siyasa.

“Ya kamata ku sani cewa bayan fuskar jin ƙai da FETO ke nunawa, akwai wata ƙungiya da ke ƙoƙarin kutsawa cikin harkokin mulki da na siyasa a ƙasashen da ta ke aiki.”
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Asalin ƙungiyar FETO da rikicin ta da Turkiyya

FETO da aka fi sani da Hizmet a harshen Turkiyya, ƙungiya ce da aka ce Fethullah Gülen ya kafa a shekarun 1950, malamin da ya rasu a watan Oktoba, 2024 a Amurka yana da shekara 83.

Kara karanta wannan

Abin da shugabannin ƙasashen duniya ke cewa game da Buhari bayan Allah ya masa rasuwa

Gwamnatin Turkiyya na zargin ƙungiyar da kitsa juyin mulkin 2016 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 250.

Bayan haka, Turkiyya ta kwace kadarorin makarantu, kamfanoni, da cibiyoyi da ke da alaƙa da FETO a duniya.

Sai dai duk da haka, ƙungiyar na musanta hannu a juyin mulkin tare da kin amincewa da kiran su ’yan ta’adda.

An kafawa Turji sharadin sulhu a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Sokoto ta yi martani bayan dan ta'adda, Bello Turji ya nuna alamun neman sulhu.

Rahotanni da Legit ta samu sun nuna cewa dan ta'addan ya fito a ciki wani bidiyo ne yana nuna alamar cewa zai iya ajiye makami.

Sai dai gwamnatin Sokoto ta yi martani da cewa idan da gaske ya ke, ya kamata a fara gani ya daina kai hari kan al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng