An Fadawa Tinubu abu 1 da Najeriya Ke Bukata bayan Mutuwar Buhari a London
- Dan rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gina asibitoci da za su dace da kiwon lafiya na duniya
- Ya ce Najeriya na bukatar asibitin zamani don dakile dogaro da kasashen waje, bayan rasuwar Muhammadu Buhari a asibitin London
- Adeyanju ya jaddada cewa aikin yana yiwuwa kafin karshen wa’adin mulkin Tinubu, idan aka nuna jajircewa da kudurin siyasa mai karfi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Dan rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakin gaggawa domin gyara tsarin kiwon lafiya a Najeriya.
Ya kuma bukaci shugaban kasar da ya gaggauta gina asibiti mai nagarta irin na duniya a cikin kasar, domin kaucewa abin kunyar da Najeriya ke fuskanta.

Source: Facebook
A shafinsa na Facebook, Adeyanju ya bayyana rashin irin wannan asibiti a Najeriya a matsayin "abin da ake bukata cikin gaggawa" da kuma "abin kunya da ya wuce kima."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarar da aka ba Tinubu bayan rasuwar Buhari
A sanarwa da ya wallafa ranar Talata, Adeyanju ya shawarci shugaban kasa Tinubu da ya fifita gyaran bangaren lafiya kafin karshen wa'adin mulkinsa.
Wannan magana ta Adeyanju ya zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu 'yan Najeriya ke korafi kan yadda aka fitar da Muhammadu Buhari waje don duba lafiyarsa kuma ya rasu a asibitin London.
'Dan rajin kare hakkin dan Adam din ya rubuta cewa:
“Mai girma shugaban kasa Tinubu, da fatan za ku gyara tsarin kiwon lafiya na Najeriya. Ku gina asibiti mai inganci a cikin Najeriya. Wannan ya kamata ya zama abin gaggawa na kasa. Abin kunyar ya yi yawa sosai.”
Adeyanju, wanda aka fi sani da tsayuwa tsayin daka kan batutuwan shugabanci, ya jaddada cewa ana iya yin irin wannan aikin idan aka sanya niyyar siyasa mai karfi.
Ya kara da cewa:
“Za a iya kammala hakan kafin karshen wa’adin mulkinku. Ku dai bayar da izini, sannan ku tabbatar an ware kudin aikin.”
An kawo bukatar kara zuba jari a fannin lafiya
Maganganun Adeyanju sun zo a daidai lokacin da damuwa ke karuwa kan rashin isasshen kayan aiki da yanayi mara kyau a asibitocin Najeriya.
Jaridar Leadership ta ce ana zargin halin da asibitocin kasar ke ciki ne ke sa jami'an gwamnati ci gaba da dogaro da asibitocin kasashen waje domin duba lafiyarsu.
A cewar rahoton, zuwan jami'an gwamnati ko 'yan siyasa waje neman lafiya ya sa masu sukar lamirin gwamnati ke kallon hakan tamkar raina ingancin cibiyoyin kiwon lafiya na gida.
Masu lura da al’amura sun ce kiran Adeyanju ya zo daidai da ra’ayin dimbin ‘yan Najeriya da ke ci gaba da rokon gwamnati da ta zuba jari a cikin cibiyoyin kiwon lafiya na gida, ta inganta kayan aiki da kuma rayuwar ma’aikatan lafiya.
Wannan kira ya sake fitowa fili ne bayan rasuwar Buhari a wani asibiti da ke birnin London ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.

Source: Getty Images
Asibitin London da Buhari ya rasu
Buhari ya rasu a "The London Clinic" da ke unguwar Marylebone, a Birtaniya, inda ya kwashe kwanaki 230 yana jinya tun lokacin mulkinsa, a cewar rahoton gidauniyar tallafawa 'yan jarida masu binciken kwakwaf (FIJ).
Asibitin, wanda ke kan titin 22 Devonshire Place a London, na daga cikin manyan asibitoci masu zaman kansu da ke kula da shugabannin siyasa, shahararrun mutane da jakadun kasashe.
A shafin FIJ na intanet, an bayyana cewa asibitin London Clinic ne Buhari ya fi yawan ziyarta idan ya je waje neman lafiya, la’akari da cewa a nan ne ya rasu, da kuma irin bayanan da hadimansa ke bayarwa a baya.
Shahararrun shugabannin duniya da masu mulki, ciki har da ‘yan masarautar Birtaniya, sun taba samun kulawa a wannan asibiti.
Shugabannin siyasa irin su tsohon shugaban Amurka, John F. Kennedy, da tsofaffin Firayim Ministocin Birtaniya, Clement Attlee da Sir Anthony Eden, sun taba jinya a wannan asibiti.
Yadda aka sauke gawar Buhari a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, filin jirgin sama na Katsina ya cika makil da jama’a a lokacin da aka sauke gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa, Kashim Shettima, da ‘yan uwa da iyalan Buhari, da kuma manyan jami’an gwamnati sun tarbi gawar a filin jirgin.
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla gwamnoni 20, ministoci, da shugabanni daga fannoni daban-daban sun isa Daura domin halartar jana’iza da binne marigayin shugaban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



