Buhari ya amince da nadin sabbin shugabanin asibitoci a Jalingo da Calabar

Buhari ya amince da nadin sabbin shugabanin asibitoci a Jalingo da Calabar

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sabbin nadi masu muhimmanci a bangaren lafiya yayin da ake yaki da coronavirus

- Shugaban kasar ya nada shugabanin asibitoci biyu a Calabar, jihar Cross Rivers da kuma Jalingo a jihar Taraba

- Sabbin shugabaanin asibitocin sun hada da Dr Bassey Eyo Edet da Dr Aisha Shehu Adamu wadanda za su fara aiki a ranar 25 ga watan Maris na 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin shugabanin asibitoci biyu; Asibitin Kwakwalwa na Calabar da ke jihar Cross Rivers da kuma Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Jalingo a jihar Taraba.

Sabbin shugabanin da aka nada, a cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a ranar Alhamis 2 ga watan Afrilu sune Dar Bassey Eyo Edet da Dr Asiha Shehu Adamu.

Buhari ya amince da nadin sabbin shugabanin asibitoci a Jalingo da Calabar
Buhari ya amince da nadin sabbin shugabanin asibitoci a Jalingo da Calabar
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

Legit.ng ta ruwaito cewa Dr Edet dan asalin karamar hukumar Akpabuyo ne a jihar Cross Rivers. Ya yi digirinsa na farko a Jami'ar Calabar a shekarar 1998.

Ya kuma yi karatu a kwallejin kiwon lafiya ta kasa da cibiyar kwararru ta National Institute of Management Consultants.

Nadin da aka masa a matsayin shugaban asibitin na wa'adin shekaru hudu zai fara ne daga ranar Laraba, 25 ga watan Maris.

Dr Aisha Shehu Adamu ita ma kwararriyar likita ce a bangaren cututtukar da suka shafi hanji da hanta. Dr Adamu yar asalin karamar hukumar Karin-Lamido ne daga jihar Taraba kuma ta kammala digirin ta na farko daga Jami'ar Maiduguri a shekarar 1995.

Nadin da aka mata a matsayin shugaban asibitin zai fara aiki ne daga ranar Laraba 25 ga watan Maris na 2020. Itama wa'adin nadin nata na shekaru hudu ne.

Legit.ng ta lura cewa shugaban kasar ya yi wannan muhimman nade-naden ne a lokacin da kasar ke yaki da annobar coronavirus da ta adabi kasashen duniya ciki har da Najeriya.

A cewar Cibiyar Kare Cututtuka masu yaduwa (NCDC) adadin wadanda suka kamu da cutar ta Covid-19 a kasar zuwa ranar Alhamis 2 ga watan Afrilu sun kai 184.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel