Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa

Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa

- Majalisar dattijai ta gargadi babban sakataren fadar shugaban kasa a kan su dakatar da shugaba Buhari daga fita ketare domin neman lafiya

- Gargadin majalisar na zuwa a lokacin da babban sakataren fadar shugaban kasa ya gabatar da kasafin fadar shugaban kasa a gaban majalisa

- Fadar shugaban kasa ta gabatar da kasafin kudinta na shekarar 2021 wanda ya kama N19.7bn

A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.

A cewar majalisar, yin hakan zai tabbatar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ya koma hayyacinsa a cikin shekarar nan.

Kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito da alaka a tsakanin bangarorin gwamnati ne ya yi wannan gargadi yayin da babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansa domin kare kasafi kudin shekarar 2021.

DUBA WANNAN: Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

Fadar shugaban kasa ta gabatar da kasafin kudinta na shekarar 2021 wanda ya kama N19.7bn, daga cikin kudin ne kuma aka warewa asibitin fadar shugaban kasa zunzurutun kudi da yawansu ya kai N1.3bn.

Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa
Majalisar dattijai
Asali: Facebook

Da ya ke martani a kan kasafin kudin, shugaban kwamitin, Sanata Danjuma La'ah, ya ce kwamitin zai amince da kasafin fadar shugaban kasa amma ya jaddada cewa shugaban kasa da sauran manyan jami'an gwamnati ba zasu kara fita waje domin a duba lafiyarsu ba.

KARANTA: Kano: Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adarta - Matar aure a gaban kotu

Da ya ke ganawa da manema labarai bayan gabatar da kasafin kudin, Umar ya dauki alkawarin samar da dukkan kayayyakin duba lafiya da shugaban kasa da sauran manyan jami'an gwamnati ke bukata a asibitin fadar shugaban kasa da zarar majalisa ta amince da kasafin kudin da ya gabatar.

A wani yunƙurin ƙarawa jami'an ƴansanda himma da karsashi a ƙasa baki ɗaya domin farfaɗowa da sauri daga illolin zanga-zangar #EndSARS, babban Sufetan ƴansanda na ƙasa ya ce dukkanin jami'an da suka rasa ransu ko suka jikkata za'a ɗaga darajarsu zuwa matsayi na gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng