'Ba Zan Bar Maku Gadon Dukiya ba,' Abin da Buhari Ya Fadawa Ƴaƴansa kafin Ya Rasu
- Muhammadu Buhari ya bayyana wa 'ya'yansa cewa ba zai bar musu gadon dukiya ba, sai dai ya karfafa musu gwiwa su nemi ilimi
- Buhari ya bayyana hakan ne a ranar 13 ga watan Yulin 2022, a ziyarar da ya kai Daura, lokacin yana rike da shugabancin Najeriya
- Kafin rasuwarsa a ranar 13 ga watan Yulin 2025, Buhari ya fadawa sarkin Daurawa irin tarbiyyar da yake so a rika yi wa 'ya'ya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - A ranar Laraba, 13 ga watan Yulin 2022, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanar da 'ya'yansa cewa ba zai bar masu gadon dukiya ba.
A lokacin, Buhari ya karfafi gwiwar ‘ya’yansa da su tashi haikan su nemi ilimi mai inganci domin su sami nasara a rayuwa, su tara arzikin da kansu.

Source: Twitter
Tinubu ya nemi a ilimantar da yara
Jaridar Tribune ta rahoto cewa Buhari ya bayyana hakan ne a Daura, jihar Katsina, kuma a ranar ne ya roƙi iyaye da su koya wa ‘ya’yansu dabi’un kirki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin dabi'un da Buhari ya yi magana a kan su akwai tsoron Allah, girmama hukuma, da kuma yin rayuwa mai ma’ana ta hanyar neman ilimi.
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa a wancan lokaci ya rawaito Shugaba Buhari ya shawarci matasa da su nemi ilimi ba domin samun aikin gwamnati ba.
A cewar Buhari, babu wani aikin gwamnati a lokacin, don haka, a nemi ilimi don samun ƙwarewa da fasaha da za a yi amfani da su wajen yakar talauci.
Shirin da Tinubu ya yi wa 'ya'yansa
Buhari, wanda ya kai gaisuwar Sallah fadar Mai Martaba Sarkin Daura, ya ce ya kamata a ba da ƙarin lokaci wajen horar da shugabannin gobe.
Ya ce za a yi hakan ne ta hanyar basu ilimi game da dabi’un kirki, ganin yadda duniya ke sauyawa da sauri a kan fasahar zamani da ke buƙatar gogewa.
Ya ƙara da cewa:
“An tsare ni fiye da shekaru uku bayan na jagoranci ƙasar. A lokacin ne na yi karatun ta-nutsu, na gaya wa ‘ya’yana cewa darajarku tana tare da abin da ke cikin kwakwalwarku, ba abin da kuka mallaka a rayuwa ba.
“Abinda na fi maida hankali a kai shi ne kula da tarbiyyar ‘ya’yana ta yadda za su iya zama masu amfani ga al'umma a duk inda suka tsinci kansu."

Source: Twitter
"Ba zan bar maku gadon dukiya ba" - Buhari
Jaridar The Cable ta rahoto wasiyyar da 'ya'yan Buhari suka samu daga mahaifinsu, inda aka ji shugaban yana cewa:
"Na gaya wa ‘ya’yana, musamman ‘yan mata, cewa ba za su yi aure ba sai sun gama karatun digiri na farko.
“Tuni sun san cewa ba zan bar musu wani abin gado na dukiya ba. Gado mafi girma da zan bar musu shi ne tabbatar da cewa sun samu ilimi mai nagarta.”
Shugaban ƙasar na wancan lokaci ya ce yana da muhimmanci a koya wa kananan yara tarihi, domin ba za su iya zama masu kishin ƙasa, nagarta da biyayya ba sai sun fahimci asalin su da tarihinsu sosai.
Muhammadu Buhari ya rasu a London
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a wani asibiti da ke birnin London.
Rahotanni sun nuna cewa Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga Yulin 2025 bayan doguwar rashin lafiya da ya sha fama da ita.
Biyo bayan hakan, Shugaba Tinubu ya kira Aisha Buhari domin jajanta mata, tare da umartar Mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya tafi London domin rako gawar marigayin.
Asali: Legit.ng


