Cikin Hotuna: Buhari ya karbi gaisuwar sallah ta manyan Najeriya a gidansa na Daura
Shafaffu da mai da kuma masu gata a Najeriya, sun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa na Daura dake jihar Katsina domin kwasar gaisuwa da taya murnar bikin babbar sallah da aka gudanar a ranar Lahadi.
Jerin wadanda suka yi tattaki har zuwa Daura domin gabatar da gaisuwa da kuma taya shugaban kasa murnar bikin babbar sallah sun hadar da tsohon gwamna, sanata, zababben minista, surukai, manyan mata, babban akanta kasa da sauransu.
Fadar shugaban kasa ta bayyana yadda 'ya'yan shugaba Buhari uku da suka hadar da Yusuf, Hanan da kuma Aminatu, suka kimtsa masa shiri gabanin karbar bakuncin wasu manya da suka kai masa ziyara har garin Daura.
Ana iya tuna cewa, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, na ci gaba da gudanar da ibada wadda ta kasance daya daga cikin rukanan musulunci wato sauke farali na aikin hajji a kasa mai tsarki.
KARANTA KUMA: Tabbatar da zaman lafiya da sauran sakonni 6 da Buhari ya yi a jawabansa na goro Sallah
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng