Ministar Kudi a Gwamnatin Buhari Ta Gina Gidan Naira Miliyan 70, Za Ta Kula da Marayu
- Tsohuwar minista, Kemi Adeosun ta kaddamar da gidan jin kai na N70m domin tallafa wa matasa da marasa galihu a Abuja
- Ta ce gidan zai zama matsugunni ga matasan da suka girmi zama gidan marayu, inda za su samu horo, ilimi da tallafin rayuwa
- Adeosun ta ce sun bude wani sabon shagon DashMe a Abuja don sayar da kaya, kuma ayi amfani da kudin don ayyukan jin-kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun, ta kaddamar da wani gida na jin kai da ta gina a Abuja da ya kai kimanin Naira miliyan 70.
Yayin bikin kaddamar da gidan, Adeosun ta yi kira ga ƴan Najeriya da su rungumi ayyukan jin kai da ke tallafa wa yara marasa galihu, matan da ke fuskantar cin zarafi da kuma masu fama da nakasa.

Source: Twitter
Tsohuwar minista ta gina gidan N70m
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a a Abuja don tunawa da cikar shekara huɗu da kafuwar gidauniyarta ta DashMe Foundation, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarta, sabon gidan da aka gina zai zama matsugunin wucin gadi ga matasa da suka manyanta daga gidan marayu amma ke buƙatar tallafi don fara rayuwa mai 'yanci.
Tshohuwar ministar kudin a gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce:
“Muna murnar wannan babban ci gaba na kammala Gidan Gidauniyar DashMe da zai amfanar da gidauniyar Sought After Women and Children.
"Wannan gida zai ba matasa masu shekaru 18 zuwa 25 mafaka mai aminci da mutunci don fara sabuwar rayuwa.”
Adeosun ta jaddada cewa yawancin marayu sukan fuskanci koma-baya a zamantakewa bayan sun kai shekaru 18, don haka ne wannan gida zai cike gibi ta hanyar bayar da horo na sana’a, ilimi, shawarwari da matsugunni.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da ke hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara
Wadanda za a rika ba mafaka a gidan
Ta bayyana cewa tsarin Gidauniyar DashMe ya ta'allaka ne kan tara kyaututtuka daga jama’a, sayar da su, sannan a yi amfani da kudin wajen tallafa wa marasa galihu.
A nata bangaren, Carol Silver-Oyaide, wacce ta kafa gidauniyar Sought After Women and Children, ta bayyana jin daɗinta bisa wannan kyauta daga Adeosun da tawagarta, tana mai bayyana gidan a matsayin babban aiki da zai sauya rayuwa.
Carol Silver-Oyaide ta ce:
“Manufarmu ita ce sauya rayuwar waɗanda aka cutar da su, waɗanda ke cikin raɗaɗi da waɗanda aka watsar. Wannan gida zai sauya rayuwar matasa da yawa.”

Source: Facebook
Yadda gidauniyar ministar ke samun kudade
A yayin bikin cikar shekara huɗu da kafuwar gidauniyar, an kuma kaddamar da sabon shagon jin kai na DashMe da ke Wuse 2, Abuja – na uku kenan bayan na Surulere da Lekki a Legas.
Shagon yana sayar da sabbin kaya da waɗanda ba su lalace ba da jama’a ke bayarwa kyauta, inda ake amfani da ribar da ake samu wajen ayyukan jin kai.
Adeosun ta bayyana cewa wannan ƙungiya da ta fara a aiki a shekarar 2021 yanzu ta zama cibiyar jin-kai a sassa daban-daban na Najeriya da kuma ƙasashen Birtaniya da Amurka.
Ta ce tasirin gidauniyar ya shafi jihohi da dama, daga birnin Legas zuwa ƙauyukan jihar Cross River har ma da Borno, inda ake tallafa wa mutanen da rikici ya raba da muhallansu.
Kotu ta wanke Kemi Adeosun kan NYSC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohuwar ministar Buhari ta bayyana farin cikinta da kotu ta wanke ta bisa zargin amfani da takardar bogi.
Kotu ta wanke Kemi Adeosun a ranar Laraba, 7 ga Yulin 2021, bayan share shekaru sama da uku kan batun zarginta da gabatar da takardar NYSC ta bogi.
Misis Kemi Adeosun ta ce, wannan ba nasara ce ga ita kadai ba, nasara ce ga dukkan 'yan Najeriya dake rayuwa a kasashen waje.
Asali: Legit.ng

