Muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabuwar Ministan Kudi, Zainab Ahmed
A jiya, Juma'a 15 ga watan Satumba ne shugaba Muhammadu Buhari ya amince da murabus din tsohuwar Ministan Kudi, Kemi Adeosun bayan an kwashe watanni ana cece-kuce kan zarginta da gabatar da certificate din kammala hidimar kasa ta bogi.
Shugaban kasa ya godewa ministan bisa gudunmawar da ta bayar a lokacin aikin ta tare da yi mata fatan alheri a ayyukan da za ta yi a gaba.
Ba tare da bata lokaci ba, shugaban kasa ya umurci karamar ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed ta maye gurbin Kemi Adeosun a matsayin ministan Kudi.
Ga wasu muhimman abubuwa 8 da ya dace ku sani a kan Zainab Ahmed.

Asali: Depositphotos
1) An haifi Zainab Shamsuna Ahmed ne a 1963 a jihar Kaduna.
2) Ta kammala karatun digiri na farko daga Jami'an Ahmadu Bello da ke Zaria a 1981 kana ta yi karatun digiri na biyu a fanin nazarin kasuwanci (MBA) a Jami'ar Jihar Ogun da ke Ago Iwoye.
3) Ta fara aiki a matsyasin Akanta a shekarar 1982 a M'aikatar Kudi na jihar Kaduna kuma daga baya ta koma Kamfanin Sadarwa na Kasa (NITEL).
4) A 1995, tayi aiki a sassa daban-daban har ta samu karin girma zuwa matsayin mataimakiyar manaja (DGM)
DUBA WANNAN: Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari
5) A shekarar 1995, an nada ta babban sakatariya a Nigeria Industries Transparency Initiative
6) Kafin a nada ta Ministan Kudi na kasa, ita ce Karamar Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Kasa.
7) Ita mamba ce ta Kungiyar Akanta na Najeriya (ANAN) kuma mamba a kungiyar Cibiyar Haraji na Najeriya.
8) A watan Mayun 2009, an nada ta babban manajan Kamfanin Saja Jari na Jihar Kaduna. An kuma nada ta mamba na Kwamitin masu bayar da shawarwari a NEITI.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng