Da duminsa: Bayan da kotu ta wanke ta kan batun NYSC, ministar Buhari ta yi martani

Da duminsa: Bayan da kotu ta wanke ta kan batun NYSC, ministar Buhari ta yi martani

  • Tsohuwar ministar Buhari ta bayyana farin cikinta da kotu ta wanke ta bisa zargin amfani da takardar bogi
  • Kotu ta wanke ta yau Laraba bayan share shekaru sama da uku kan batun zarginta da gabatar da takardar NYSC ta bogi
  • Ta ce, wannan ba nasara ce ga ita kadai ba, nasara ce ga dukkan 'yan Najeriya dake rayuwa a kasashen waje

Wata tsohuwar Ministar Kudi Misis Kemi Adeosun ta ce wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta tabbatar da gaskiyarta, The Nation ta ruwaito.

Amma duk da haka ta yarda da cewa ta yi matukar bakin ciki game da zarginta da gabatar da takardar NYSC ta bogi.

Ta ce hukuncin da Justis Taiwo Taiwo ya yanke ba nasara ce kawai gare ta kadai ba, nasara ce ga dukkan ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Ta ce za ta kara daukar matakai a lokacin da ya dace don kare mutuncinta.

KARANTA WANNAN: Jami'a a Najeriya ta ce dole dalibai su fara sanya 'Uniform', dalibai sun yi turjiya

Da duminsa: Bayan da kotu ta wanke ta kan batun NYSC, ministar Buhari ta yi martani
Tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Bayan zargin gabatar da takardar shaidar bautar kasa ta NYSC ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da Majalisar Dokoki ta Kasa don neman tantancewa, tsohuwar Ministar a ranar 14 ga Satumba, 2018 ta yi murabus daga mukaminta.

Amma ta nemi lauyoyi don su fafata a madadinta a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.

Kotun a ranar Laraba ta ce bai kamata tsohuwar Ministar ta gabatar da kanta ga shirin hidima ta NYSC ba tun farko.

Da take martani kan wanke ta da kotun tayi, Legit.ng Hausa ta tattaro Adeosun na cewa:

“Hukuncin ya wanke ni bayan wani mummunan yanayi da na shiga. Duk da haka, ba nasara ta ba ce kawai; wannan nasara ce ga dukkan ‘yan Najeriya dake kasashen waje dake cikin irin wannan yanayi wadanda ke da muradin yi wa kasarsu hidima.
“Ina so in godewa Allah, iyalina, abokai na, mashawarcina, Cif Wole Olanipekun (SAN) da kuma masu yi min fatan alheri saboda kauna, kulawa da kuma nuna damuwarsu tsawon wannan mawuyacin lokacin da ya dauki shekaru uku.
“Ina so in kara dangane da hukuncin kotu, zan yi komai a lokacin da ya dace ba tare da wata damuwa ba, in dauki dukkan matakan da suka dace na doka don kare mutuncina. Ina godiya gare ku duka.”

Kotu ta wanke tsohuwar ministan Buhari kan badakalar kwalin NYSC

Tsohuwar ministan kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli ta wanku a gaban kotu kan zarginta da ake da kin yi hidimar kasa ta NYSC.

Kamar yadda alkali mai shari'a, Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya yanke, bai dace ta yi hidimar kasan ba koda ta kammala digiri a shekaru 22 saboda har a lokacin 'yar Birtaniya ce, The Nation ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Iyayen daliban Bethel sun fusata, sun fatattaki kwamishinan El-Rufai a yankinsu

Kotun ta kara da cewa tsohuwar ministan ta dawo kasarta ta gado lokacin da ta wuce shekaru 3 a duniya, lamarin da yasa ba za ta iya hidimar kasa ba.

Har ila yau, Mai shari'a Taiwo ya ce wacce ake karar bata bukatar shaidar kammala NYSC kafin a nadata a matsayin minista a Najeriya, Leadership ta kara da cewa.

Batun Daukaka Magu: PDP ta zargi shugaba Buhari da goyon bayan cin hanci da rashawa

A wani labarin, Jam’iyyar PDP ta yi tir da kakkausar murya game da shirin da fadar shugaban kasa ta yi na daukaka tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu zuwa rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF).

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun yadu a kafafen watsa labarai na yanar gizo cewa za a tura Magu zuwa ofishin Mataimakin Sufeto-Janar (AIG) ta Hukumar Kula da 'Yan sanda (PSC), The Cable ta rahoto.

Da take bayyana matakin da ake yadawa a matsayin wuce gona da iri, PDP a wata sanarwa a ranar Talata, 6 ga watan Yuli, ta ce hakan cin fuska ne ga idon 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel