Duk da Hukuncin Kotu, Sanata Natasha Ta Rasa Babban Mukaminta a Majalisar Dattawa

Duk da Hukuncin Kotu, Sanata Natasha Ta Rasa Babban Mukaminta a Majalisar Dattawa

  • Majalisar dattawa ta sauke Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga shugabancin kwamitin 'yan gudun hijira da kungiyoyin sa-kai
  • Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya maye gurbin Natasha da Sanata Aniekan Bassey a matsayin sabon shugaban kwamitin
  • Yayin da kotu ta umarci majalisar majalisar da ta mayar da Natasha bakin aiki, majalisar ta nace cewa ba ta samu kwafin hukuncin ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Majalisar dattawa ta cire Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga muƙamin shugabar kwamitin majalisar kan harkokin 'yan gudun hijira da kungiyoyin sa-kai.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya naɗa Sanata Aniekan Bassey a matsayin sabon shugaban kwamitin, inda ya tabbatar da maye gurbin Sanata Natasha.

Sanata Godswill Akpabio ya kwace shugabancin kwamitin majalisar dattawa daga hannun Sanata Natasha
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta rasa shugabancin kwamitin majalisar dattawa. Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Majalisa ta kwace mukamin Sanata Natasha

Sanata Aniekan Bassey shi ne dan majalisar dattawan da ke wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Akpabio ya nada Sanata Natasha shugabar kwamitin harkokin 'yan gudun hijira da kungiyoyin sa-kai ne a watan Fabrairun 2027.

An yi mata nadin ne bayan an cire ta daga muƙamin shugabar kwamitin majalisar kan harkokin ci gaban fasahohin gida a wani ƙaramin sauyi da aka yi.

Ko da yake ba a bayar da dalilin cire Natasha ba a zaman majalisar na ranar Alhamis, amma an yi imanin cewa wannan sauyin yana da alaƙa da dakatarwar da aka yi mata.

Jaridar Vangaurd ta ce yanzu Sanata Natasha za ta koma majalisar ne ba tare da wani mukami na shugabantar kwamitin majalisar dattawan ba.

Hukuncin kotu kan dakatarwar Sanata Natasha

A farkon Yulin 2025, Mai Shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya ta ba da umarnin mayar da Sanata Natasha kan muƙaminta tare da umartar ta da ta nemi afuwa ga majalisar dattawan.

Sai dai, majalisar dattawa ta nace cewa ba ta samu ingantaccen kwafin hukuncin kotun ba har yanzu, balle a yi maganar ko za a iya mayar da ita bakin aiki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kira gwamna, tsofaffin gwamnoni da jami'an tsaro kan kashe kashe

Har yanzu, Sanata Natasha, wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, ba ta koma bakin aikinta na majalisa ba duk da hukuncin kotu da ya soke dakatarwarta.

A wata hira da aka yi da ita a ranar Talata, ta ce tana jiran ingantaccen kwafin hukuncin kotun kafin ta koma zauren majalisa a hukumance.

Sanata Natasha ta ce an hana al'ummar mazabar Kogi ta Tsakiya murya saboda hana ta komawa aiki a majalisa
Sanata Natasha H Akpoti, 'yar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya. Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Tasirin dakatarwar Natasha ga mazabarta

Ko da yake kotu ta bayyana dakatarwarta a matsayin “zarce laifin da ta yi da kuma sabawa kundin tsarin mulki”, majalisar ta ce hukuncin kotun bai hana a ladabtar da Natasha ba

Sanata Natasha, ɗaya daga cikin sanatoci mata uku kacal a majalisar ta yanzu, ta ce ci gaba da jinkirta komawarta bakin aiki wata babbar barazana ce ga majalisar da aka ginata a kan dimokuradiyya.

Yayin da ta ce ci gaba da rashin wakiltar al'ummar mazabarta a majalisar ya take hakkinta, Sanata Natasha ta kuma ce:

“Ta hanyar hana ni shiga zauren majalisa, majalisar dattawa ta rufe bakin 'yan mazabar Kogi ta Tsakiya, kuma ta hana mata wakilci. Sanatoci mata uku ne kacal yanzu a majalisar."

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, tsohon shugaban majalisar wakilai ya rasu

Sanata Natasha ta sanar da ranar komawa aiki

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta ce za ta koma zauren majalisar dattawa a wannan makon.

Wannan na zuwa ne bayan kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci cewa dakatarwar watanni shida da aka yi mata ta saba ka'ida, kuma ta take hakkinta da na mazabarta.

Sai dai kotun ta kuma ci tarar Sanatar saboda ta karya wasu ka’idojin da aka shimfiɗa a yayin shari’ar da ta shigar da Majalisar Dattawan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com