Plateau: Batun Kisan Ƴan Zaria Ya Dawo, an Gurfanar da Mutum 22 bayan Gama Bincike

Plateau: Batun Kisan Ƴan Zaria Ya Dawo, an Gurfanar da Mutum 22 bayan Gama Bincike

  • 'Yan sanda a Jihar Plateau sun fara gurfanar da mutum 22 da ake zargi da hannu a kisan baki 13 'yan daurin aure a Mangun
  • Kwamishinan 'yan sanda Emmanuel Adesina ya ce an kama wadanda ake zargi bayan hadin gwiwa da jami'an tsaro
  • Adesina ya bukaci matasa su guji daukar doka a hannu, ya ce duk wanda ke da hannu zai fuskanci hukunci cikin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Plateau ta kammala bincike bayan kisan yan Zaria a jihar.

Rundunar ta fara shari’ar mutum 22 da ake zargi da kisan bak’i 13 a unguwar Mangun a karamar hukumar Mangu.

An gurfanar da yan Plateau a kotu kan kisan yan Zaria
Yan sanda sun tura matasa da suka kashe yan Zaria kotu a Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Facebook

Plateau : An gurfanar da mutane 22 a kotu

Rahoton Punch Online ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Yuni, 2025, bayan da wani motar haya daga Kaduna ta fuskanci farmaki.

Kara karanta wannan

Ba rufa rufa: Za a fito da 'yan Filato da suka kashe Hausawan Zariya fili a kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana da manema labarai a hedkwatar rundunar a Jos, Kwamishina Emmanuel Adesina ya ce sun dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin.

Ya ce bincike ya kammala kuma wadanda ake zargi za su fuskanci shari’a domin tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Kwamishinan ya ce:

“A ranar 20 ga Yuni, 2025, mun samu rahoton cewa wata motar haya daga Kaduna na fuskantar farmaki a kasuwar Mangun.
“Bayan samun rahoton, na umarci DPO na Mangu da ya jagoranci jami’ai zuwa wurin don dakile lamarin.
“Da isarsu wurin, tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, sun tarwatsa mutanen da suka farma motar kuma sun ceci mutane 21."

Ya ce binciken farko ya nuna cewa bak’in sun fito ne daga Zariya, suna hanyarsu ta zuwa bikin aure a garin Kwa, karamar hukumar Qua’anpan, cewar Leadership.

Mutanen na cikin wata babbar motar daukar fasinja mai dauke da tambarin Ahmadu Bello University, Zaria, inda suka bace hanya suka fada hannun farmakin.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sun gwabza fada da 'yan bindiga a Katsina, an rasa rayuka 36

Yan sanda sun ɗauki mataki kan matasa a Plateau
An tura mutum 22 kotu bayan kisan baki a Plateau. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Alkawarin yan sanda ga al'ummar Plateau

Adesina ya bayyana cewa ya tura jami’an sashen bincike da na leken asiri zuwa Mangu domin zurfafa bincike da tattara bayanai.

Ya ce:

“Na kuma tura rundunonin kwararru da sauran sassan tsaro don kama duk wanda ke da hannu a wannan mummunan aiki.
“A ranar 21 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 7 na safe, na kai ziyara wurin tare da manyan jami’an rundunar da na sauran hukumomin tsaro.
“Ina farin cikin sanar da cewa mun kama mutum 22 yayin da sauran guda shida ke tsere.”

Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar Plateau cewa rundunar na bakin kokari don ganin wadanda ke da hannu sun fuskanci hukunci.

Ya shawarci matasa da su guji daukar doka a hannunsu, su rika kai rahoton duk wani abin zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Kisan baki a Plateau: Uba Sani ya yi ta'aziyya

Kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kai ziyarar ta'aziyya kan kisan da aka yi wa ƴan ɗaurin aure a Plateau.

Kara karanta wannan

An gwanza fada a Filato, an kashe 'yan banga 70 da kona gidaje

Uba Sani ya shawarci takwarorinsa gwamnoni da su kare ƴancin da ƴan ƙasa suke da shi na zuwa duk inda suke so.

Gwamnan ya yabawa mutanen Basawa kan rashin ɗaukar doka a hannunsu sakamakon kisan gillar da aka yi wa ƴan uwansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.