Sokoto, Kaduna da Jihohin Arewa 8 Za Su Fuskanci Ruwan Sama da Tsawa a Ranar Laraba
- NiMet ta gargadi jama'a kan yiwuwar afkuwar ambaliya sakamakon ruwan sama mai yawa da tsawa da zai iya sauka a sassan Najeriya
- Ana sa ran jihohin Arewa kamar Taraba, Sokoto, da Kaduna za su fuskanci ruwan sama mai ƙarfi da tsawa a safiya da yammacin Laraba
- Arewa ta Tsakiya da Kudu ma za su fuskanci ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi, inda NiMet ta shawarci jama'a su ɗauki matakan kariya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta ce akwai yiwuwar yawancin sassan ƙasar su samu ruwan sama da tsawa a ranar Laraba, 9 ga Yulin 2025.
Hukumar ta yi gargadi ga jama'a da su kasance cikin shiri domin ta hango yiwuwar barkewar ambaliyar ruwa da kuma rushewar gidaje a wasu yankuna.

Kara karanta wannan
‘Ku Ƙaura’: Ambaliya za ta yi ɓarna a Sokoto, Yobe, Neja da jihohi 17 a watan Yuli

Source: Getty Images
NiMet ta fitar da wannan hasashen yanayin na ranar Laraba ne a shafinta na X, inda ta bayyana cikakken yanayin saukar ruwan sama a jihohin Arewa, da Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arewa: Ruwa mai karfi hade da tsawa
Rahoton NiMet ya nuna cewa za a iya samun tsawa tare da ruwan sama mai ƙarfi a sassan jihohin Taraba, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, da Bauchi a safiyar Laraba.
A irin wannan lokacin, NiMet ta yi hasashen cewa sauran yankuna za su kasance cikin yanayin rana tare da ɗan hadari.
Da yammacin ranar zuwa dare kuwa, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a jihohin Adamawa, Taraba, Kaduna, Zamfara, Kebbi, Bauchi, Sokoto, da Gombe.
Hasashen jihohin Arewa ta Tsakiya
A safiyar ranar Laraba, ana sa ran za a samu yanayi mai rana tare da ɗan hadari a jihohin Arewa ta tsakiya.
Sai dai, rahoton hukumar NiMet ya nuna cewa za a iya samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a faɗin yankin.
Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi zai ci gaba da sauka a yawancin sassan yankin.

Source: Getty Images
Ana sa ran ruwan sama mai yawa a Kudu
A safiyar ranar Laraba a jihohin Kudu, ana sa ran hadari zai hadu tare da saukar ruwan sama a sassan jihohin Ogun, Edo, Osun, Ondo, Imo, Abia, Enugu, Bayelsa, Lagos, Delta, Cross River, Akwa Ibom, da Rivers.
Da yammaci zuwa daren ranar, NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a yawancin sassan waɗannan jihohin.
NiMet ta shawarci jama'a da su kasance cikin shiri don yiwuwar ambaliyar ruwa da kuma matsalolin da gidaje za su iya samu sakamakon tsawa da ruwa mai yawa.
An buƙaci jama'a da su ɗauki matakan kariya da kuma guje wa wuraren da ke da haɗarin ambaliya.
Ana fargabar ambaliya a jihohi 20 a Yuli
Tun da fari, mun ruwaito cewa, NiMet ta fitar da gargadi ga jihohi 20 kan yiwuwar ambaliyar ruwa a watan Yuli 2025, inda Sokoto ta fi fuskantar haɗari a matakin kololuwa.
Hukumar ta bayyana jihohin Kaduna, Zamfara, Yobe da wasu jihohi 16 a matsayin wuraren da ambaliya za ta iya shafa cikin watan, bisa ga hasashen yanayi.
NiMet ta shawarci jama’a da su tsaftace hanyoyin ruwa, su guji tuki yayin ruwa mai yawa, tare da yin kaura daga wuraren da ambaliya ke barazana.
Asali: Legit.ng

