Gwamna Ya Wanke Fulani, Ya Fadi Masu kai Hare Hare a Jiharsa

Gwamna Ya Wanke Fulani, Ya Fadi Masu kai Hare Hare a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya taɓo batun matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a yankin Kudu maso Gabas
  • Soludo ya bayyana ba Fulani makiyaya ba ne ke aikata laifukan satar mutane da kashe-kashe a yankin ba
  • Ya ɗora alhakin aikata laifukan da suka shafi garkuwa da mutane da kashe-kashe a kan ƴan ƙabilar Igbo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya wanke Fulani makiyaya kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar.

Gwamna Soludo ya bayyana cewa mafi yawan sace-sace da kisan gillar da ke faruwa a Anambra da sauran jihohin Kudu maso Gabas na Najeriya, ƴan ƙabilar Igbo ne ke aikata su.

Gwamna Soludo ya wanke Fulani kan rashin tsaro
Gwamna Soludo ya ce ba Fulani ke aikata laifuka a Kudu maso Gabas ba Hoto: Prof. Chukwuma Soludo
Source: Facebook

The Punch ta ce Soludo ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ƴan asalin jihar Anambra da ke zaune a ƙasashen waje, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Metro Points Hotel da ke New Carrollton, Maryland, Amurka.

Kara karanta wannan

Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Soludo ya ce ba Fulani ke kai hare-hare ba

Gwamna Soludo ya bayyana cewa masu aikata laifukan ba Fulani makiyaya ba ne kamar yadda ake yawan zargi ba, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

"Kaso 99.99% cikin 100% na masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka da aka kama a jihar tun lokacin da na hau kan mulki shekara uku da suka gabata, ƴan ƙabilar Igbo ne."

- Gwamna Chukwuma Soludo

Gwamnan ya shafe wasu kwanaki a Amurka tun daga ranar Lahadi yana ganawa da ƴan asalin jihar domin gabatar da cikakken rahoto kan yadda mulkinsa ya kasance a cikin shekaru uku, da nasarori da ƙalubale da gwamnatinsa ke fuskanta.

Gwamna Soludo ya ƙaryata abin da ya kira labari mai haɗari kuma mai ɓata gaskiya kan ɗora alhakin laifuka a kan Fulani Makiyaya.

"Ba Fulani makiyaya ba ne ke addabar Kudu maso Gabas, sai dai ƴan asalin yankin da ke aikata miyagun laifuka."

Kara karanta wannan

Mutane sun yi wa ɗan Majalisa rubdugu da ya kwatanta hatsarin jirgin 2006 da haɗakar ADC

- Gwamna Chukwuma Soludo

Soludo ya nuna yatsa ga masu neman ƴanci

A cewarsa, da yawa daga cikin waɗanda ke iƙirarin cewa su masu fafutukar neman ƴancin kai ne da ke ɓoye a dazuka, matasa ne ƴan Igbo da ke aikata laifuka masu nasaba da tashin hankali da kuma neman kuɗi ta hanyar haramun.

Soludo ya yi magana kan rashin tsaro
Soludo ya ce 'yan kabilar Igbo ke kai hari a Kudu maso Gabas Hoto: Prof. Chukwuma Soludo
Source: Twitter
"Mu daina ruɗar kanmu. Ku tambayi kanku, ta yaya waɗanda ake kira ƴan fafutukar yanci ke rayuwa a ɗazuka na watanni da watanni ba tare da samun tallafi daga cikin gida ba? Su waye ke ciyar da su?”
"Ina kan mulki har tsawon shekaru uku da wata uku, kusan duk wanda muka kama da laifin garkuwa da mutane ko aikata laifi, ƴan ƙaɓilar Igbo ne."
"Ƴan ƙabilar Igbo ne ke sace ƴan uwansu kuma suna kashe su, ba Fulani makiyaya ba ne. Anambra tamu ce gaba ɗaya. Ci gabanmu nauyi ne da muka ɗauka tare."

- Gwamna Chukwuma Soludo

Ya kuma yi kira ga ƴan asalin jihar da ke ƙasashen waje da su rungumi tsarin “ka tuna da gida”, su zuba jari a jiharsu ta asali kuma su bayar da gudunmawa da ƙwarewarsu da dukiyarsu domin gina jihar.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya tabbatar da cewa APC na son jawo Kwankwaso daga NNPP

Gwamna Soludo ya musanta zuwa wajen boka

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya musanta batun cewa ya ziyarci boka don zaɓen jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa babu komai a cikin jita-jitar hakan face tsabagen ƙarya mara tushe ballantana makama.

Kalaman na Soludo na zuwa ne a yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar wanda za a gudanar a watan Nuwamban 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng