Tashin Hankali: An Harbe Sojan Najeriya har Lahira a Kogi, An Samu Karin Bayanai
- Masu garkuwa da mutane sun kai sun kashe wani sojan Najeriya a harin da suka kai wani wurin gini a Ogaminana da ke jihar Kogi
- An ce bayan 'yan bindigar sun kashe sojan, sun sace ɗan kasar China a wurin da ake ginin kuma sun yi yunkurin tserewa da shi
- Sai dai kuma, jami'an tsaron hadin gwiwa sun bi bayan 'yan ta'addar, inda har hakan ya tilastawa miyagun sakin wanda suka kama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari wani wurin gini a Ogaminana, ƙaramar hukumar Adavi ta Jihar Kogi, a safiyar Litinin.
A yayin da suka kai harin, an rahoto cewa miyagun sun kashe sojan Najeriya guda daya tare da yin garkuwa da wani ɗan kasar China.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe soja a Kogi
Sojan yana kan aikin tsaro ne lokacin da waɗannan 'yan bindiga suka shiga wurin da mota, suka buɗe masa wuta da sauran waɗanda ke kan aiki, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan sun yi nasara a kan jami'an tsaro, masu garkuwar sun shiga ofishin masu kula da aikin ginin kai tsaye inda suka sace ɗan kasar Chinan.
Dan kasar Chinan, wanda ba a samu cikakken sunansa ba, ya samu raunin harbin bindiga yayin musayar wuta tsakanin masu garkuwar da jami'an tsaro.
An ce masu garkuwar, waɗanda adadinsu ya kai biyar, sun fice daga harabar wajen ginin, inda suka tsaya a tashar Radio Kogi Booster, da ke Otite.
Rahoto ya nuna cewa sun fita daga cikin motar tare da wanda suka yi garkuwa da shi, sannan suka cinnawa motar wuta suka shiga daji da gudu.
Yadda dan China ya kubuta daga 'yan bindiga
Tashar Radio Kogi Booster, Otite, tana da 'yan mitoci kaɗan daga wurin ginin inda suka sace ɗan kasar Chinan.
Wata majiya ta ce, jami'an haɗin gwiwa da suka hada da sojoji, ƴan sanda, da maharba sun isa wurin, bayan samun rahoto, kuma sun bi sahun masu garkuwar.
Majiyar ta ce:
“Har yanzu jami'an tsaron haɗin gwiwa har suna bincike a dajin da ke a kusa da inda abin ya faru domin kama masu laifin.”
An ce 'yan bindiga sun gudu sun bar ɗan kasar Chinan yayin da suka fahimci jami'an tsaron na kokarin cimmasu.

Source: Original
Bukatar karin jami'an tsaro a Ogaminana
Wata majiyar tsaro da ta yi magana kan lamarin ta ce:
"Sojojin da ke kan aiki a wajen ginin sun yi iya bakin ƙoƙarinsu don dakile harin masu garkuwa da mutanen, amma sun fi su yawa, don haka aka fi karfinsu."
“Akwai buƙatar hukumomi su tura ƙarin jami’ai zuwa yankin da sauran wuraren da ke fama da matsalolin tsaro, musamman hare-haren 'yan bindiga."
Lokacin da aka tuntubi kakakin 'yan sandan Kogi, SP William Ovye Aya, ya ce yana jiran rahoton daga babban jami'in 'yan sandan yanki (DPO), don samun cikakken bayani game da lamarin.

Kara karanta wannan
Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya
'Yan bindiga sun kashe babban sojan Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun hallaka Kyaftin Ibrahim Yohana, wani hazikin jami'in soja, watanni tara kacal bayan ya yi aure.
An yaba wa Kyaftin Yohana, ɗan asalin jihar Kaduna, bisa jajircewarsa da kishin ƙasa, kasancewarsa a sahun gaba wajen yakar masu tayar da zaune tsaye.
Rasuwarsa ta kara nuna irin barazanar da dakarun Najeriya ke fuskanta a kullum yayin da suke bakin aiki domin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.
Asali: Legit.ng

