An sace wani dan kwangilar kasar China a Zamfara

An sace wani dan kwangilar kasar China a Zamfara

Wasu 'yan bindiga da ba'a gano ko su wanene ba sun sace wani dan kasar China mai suna Ren Dajun a kusa da wata ma'aikatar ban ruwa dake kauyen Amumu a karamar hukumar Bakura na jihar Zamfara.

Dajun ma'aikaci ne a wata kamfanin kasar China wadda ta kware kan hakkar ma'adinai dake aiki a kauyen Birnin Tudu dake karamar hukumar Bakura.

Yan bindigar sun tsayar da motar da Mr Dajun ke ciki kuma suka bukaci tafintar kasar China ya fito. Bayan ya fito sun umurci ya hau kan babur sannan su kayi gaba dashi.

An sace wani dan kwangilar kasar China a Zamfara
An sace wani dan kwangilar kasar China a Zamfara

DUBA WANNAN: Majalisa ta fada cikin rudani bayan Sanatan APC ta zargi Majalisar da fifita Sanatocin PDP

Kakakin hukumar Yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu yaci jami'an hukumar na musamman masu yaki da garkuwa da mutane sun bazama aiki don ganin an ceto ma'aikacin cikin koshin lafiya tare da kama wadanda suka sace shi.

Ya shawarci al'umma sun kasance masu lura da kansu kuma su rika kai karar duk wani abinda basu amince dashi ba don a gudanar da bincike kansa.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku labarin wani hakimi, Ibrahim Madawaki wanda ya sadaukar da rayursa don ya tabbatar al'ummarsa sun kasance cikin lafiya.

Yan bindiga ne suka mamaye kauyen na Kucheri kuma suka bukaci hakimin ya hau babur ya bi su amma yaki amincewa, hakan yasa suka fara dukkansa amma sai ya nemi alfarmar cewa idan kashe shi zasuyi, su aikata hakan amma su kyale mutanensa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164