‘Ku Ƙaura’: Ambaliya Za Ta Yi Ɓarna a Sokoto, Yobe, Neja da Jihohi 17 a Watan Yuli
- Hukumar NiMet ta gargadi jihohi 20 game da yiwuwar ambaliyar ruwa a watan Yuli 2025, inda Sokoto ke cikin matsanancin haɗarin ambaliyar
- Hukumar ta lissafa Kaduna, Zamfara, Yobe, da sauran jihohi 16 a matsayin jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a cikin wannan wata
- NiMet ta ba da shawarwari kan tsaftace magudanan ruwa, guje wa tuki yayin da ake ruwa, da yin kaura daga wuraren da ambaliya za ta shafa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da gargadi ga al'ummar ƙasar game da yiwuwar ambaliyar ruwa a watan Yuli na shekarar 2025.
Hukumar ta bayyana cewa, bisa ga hasashen yanayi na kakar ruwa (SCP), akwai manyan yankuna da ke fuskantar barazanar ambaliya.

Source: Facebook
Jihohohi 20 na cikin haɗarin ambaliyar ruwa
NiMet ta lissafa jihohin Najeriya 20 da za su iya fuskantar ambaliya a sanarwar hasashen da ta fitar a shafinta na X a ranar Litinin, 7 ga Yuli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar da NiMet ta fitar, jihar Sokoto ce ke kan gaba a jerin jihohin da ke cikin haɗarin gaske na fuskantar ambaliyar ruwa.
Wannan yana nuna bukatar gaggawa ga mazauna jihar da hukumomin yankin da su ɗauki matakan kariya daga afkuwar mummunar ambaliya.
Bayan jihar Sokoto, akwai wasu jihohi 19 da NiMet ta lissafa a matsayin wadanda za su iya gamuwa da ambaliyar
Jihohin da ke fuskantar matsakaicin haɗarin ambaliya
- Kaduna
- Zamfara
- Yobe
- Bauchi
- Bayelsa
- Jigawa
- Adamawa
- Taraba
- Niger
- Nasarawa
- Benue
- Ogun
- Ondo
- Lagos
- Delta
- Edo
- Cross River
- Rivers
- Akwa Ibom
Wannan jerin ya shafi jihohi da dama a sassan ƙasar, wanda ke nuna cewa ambaliyar ruwa na iya zama babbar barazana ga yankuna daban-daban a cikin watan Yuli.

Kara karanta wannan
An shiga firgici a Gombe: Mutane 4 sun mutu, gidaje 171 sun rushe sakamakon ambaliya
Shawarwari daga NiMet don kare kai
Domin rage illolin ambaliyar ruwa, NiMet ta ba da shawarwari masu muhimmanci ga jama'a:
1. Tsaftace magudanan ruwa: A tabbatar da cewa an kwashe magudanan ruwa a yankunan gidaje da muhallai don hana taruwar ruwa.
2. A guji tuƙi ko zirga-zriga idan ana ruwa: Kada a yi tuƙi ko tafiya a cikin ruwan da ake sa ran zai haifar da ambaliya, a cewar NiMet zai iya zama mai haɗari.

Source: Getty Images
3. A kaura idan babu mafita: Idan aka ga alamar haɗarin ambaliya a waje, to a gaggauta yin ƙaura zuwa wuri mafi aminci.
4. A tanadi kayayyakin bukatu: NiMet ta bukaci jama'a su tanadi kayan bukatu na gaggawa kamar su abinci, ruwa, kayan agajin lafiya, da takardu masu muhimmanci.
5. Kashe lantarki da gas: A kashe wutar lantarki da gas din girki nan take idan aka ga alamun ambaliyar ruwa.
6. Ƙarfafa rigakafin zaizaya: A ɗauki matakai don hana zaizayar ƙasa, musamman a yankunan da ke da tudu.
7. Wayar da kan al'umma: A haɓaka wayar da kan jama'a game da haɗarin ambaliyar ruwa da matakan kariya.
8. Ɗaukar mataki da wuri: Kada a jira har lamarin ya yi muni kafin a ɗauki mataki.
Don samun ƙarin bayani, jama'a za su iya ziyartar shafin NiMet a www.nimet.gov.ng ko kuma su bi shafukan su na sada zumunta.
Manyan Arewa sun ba da mafita kan ambaliya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar ACF ta ja hankalin gwamnati kan buƙatar ɗaukar matakan kariya tun kafin ambaliyar da ake hasashen zata faru a daminar bana.
Shugabannin Arewa sun bukaci gwamnati a matakin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi da su shirya tsaf don rage illar ambaliya.
ACF ta kuma shawarci mazauna yankunan da ke cikin haɗarin ambaliya da su kiyaye muhalli, su guji toshe hanyoyin ruwa da kuma gyara gidajensu.
Asali: Legit.ng

