Katsina: Biki Ya Koma Makoki bayan Bindige Ɗan Shekara 10, an Harbi Budurwa a Kwankwaso
- Harbin bindiga ya auku a wajen bikin aure a Unguwar Liman, Magama Jibia, Katsina, inda yaro dan shekara 10 ya rasa ransa
- Wani mamba na kungiyar masu farauta ya harba bindiga wanda ya hallaka yaron Malam Yusuf, ya jikkata Shamsiyya Salisu mai shekara 25
- Rundunar ‘yan sanda ta cafke Adamu Idris da ake zargin ya yi harbin da bindigar toka, an kwato harsashi daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Wani bikin daurin aure ya koma jimami a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani yaro mai shekaru 10 ya mutu sanadin harbin bindiga ana tsaka da bikin.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa lamarin ya auku yayin bikin aure a Unguwar Liman, Magama Jibia da ke jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kura- kurai da ake samu na harba bindiga
Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun kuskure daga wasu yan banga da ke hallaka mutane duk da ana kyautata zaton ba da gangan ba ne.
Ba yan banga kadai ba har jami'an tsaro a Najeriya na samun irin wannan kuskure wanda ke jawo rashin hankali a tsakanin mutane.
Hakan ke sa ake daukar mummunan mataki idan hakan ta faru domin tabbatar da kare afkuwar matsalar a gaba.
An hallaka yaro yayin biki a Katsina
Majiyar da muka samu ta ce harbin bindigar ya hallaka yaron dan shekara 10 inda wata yarinya ta samu rauni.
Lamarin ya faru a ranar 7 ga Yuli da misalin karfe 2:50 na rana a bikin aure na daya daga cikin mambobin kungiyar mafarauta.
An ce wani mutum mai shekara 45 mai suna Adamu Idris ya harba bindigar toka yayin shagalin, harsashin ya samu Yusuf a ciki.
Harsashin ya kuma jikkata wata yarinya mai suna Shamsiyya Salisu ‘yar shekara 25 a kunkuminta, lamarin da ya girgiza mahalarta bikin.

Source: Original
Matakin da yan sanda suka dauka da gaggawa
‘Yan sanda daga ofishin Jibia sun isa wurin cikin gaggawa, aka garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa Asibitin Gwamnati na Jibia.
A can ne likita ya tabbatar da mutuwar Malam Yusuf, yayin da aka fara ba Shamsiyya kulawa a halin yanzu a asibitin.
An cafke wanda ake zargi, Adamu Idris, nan take, kuma an kwato bindigar da harsashi daya.
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa bincike ya fara, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala binciken.
Dan banga ya harbi matashi a Borno
Mun ba ku labarin cewa an harbe wani matashi da bindiga a lokacin bikin naɗin sarauta a Gwoza, jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne ana bikin nadin sarauta inda Yusuf Ahmadu ya harbe Isa Ali da gangan lokacin da ya karɓi bindiga daga wani jami'in sa-kai, Buba Hamman a wurin bikin.
An kai wanda aka harba asibitin Gwoza, likitoci suka tabbatar da mutuwarsa inda yan sanda sun kama Ahmadu da Hamman don bincike.
Asali: Legit.ng

