Bayani kan Taron BRICS da Tinubu Ya Je Brazil da abin da Ya Fada a madadin Najeriya

Bayani kan Taron BRICS da Tinubu Ya Je Brazil da abin da Ya Fada a madadin Najeriya

An gudanar da taron kasashen BRICS na 2025 a kasar Brazil, kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi a madadin Najeriya.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Brazil – Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron BRICS na 2025 a Brazil, inda ya bayyana bukatar sake fasalin tsarin shugabancin duniya da na tattalin arziki da lafiya.

Taron na shekarar 2025 ya gudana ne a birnin Rio de Janeiro, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi duniya.

Shugabannin duniya yayin taron BRICS na 2025
Shugabannin duniya yayin taron BRICS na 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa game da BRICS da bayanin da Bola Tinubu ya yi a taronsu na 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin kafuwar BRICS da yadda ta fadada

Rahoton BBC ya nuna cewa kungiyar BRICS ta fara ne da kasashen Brazil, Rasha, Indiya da China a shekarar 2006, inda daga baya Afirka ta Kudu ta shiga a 2010.

Kara karanta wannan

'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa

Manufar kungiyar ita ce hada manyan kasashe masu tasowa domin su kalubalanci karfin tattalin arziki da siyasar kasashen Turai da Amurka.

Tinubu na shan hannu da wani shugaba a wani taron BRICS na 2025
Tinubu na shan hannu da wani shugaba a wani taron BRICS na 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A farkon shekarar 2024, BRICS ta gayyaci mambobi guda biyar daga kasashen Masar, Habasha, Iran, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Najeriya ta zama abokiyar BRICS

Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa Najeriya ta zama abokiyar huldar BRICS a watan Janairu 2025, tare da Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda da Uzbekistan.

Wannan matsayi na musamman ya biyo bayan taron BRICS na 2024 da aka gudanar a Kazan, Rasha, inda aka kirkiro tsarin abokan hulda.

Tinubu a taron BRICS na 2025
Tinubu a taron BRICS na 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Najeriya ta samu wannan damar ne saboda matsayinta a Afirka da tasirinta a tattalin arzikin nahiyar.

Tinubu ya bayyana matsayinsa a BRICS

A jawabinsa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na goyon bayan manufofin BRICS, musamman na adalci, hadin kai da cigaban da ya shafi kowa da kowa.

Shugaban kasan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"Najeriya na tare da sauran mambobin BRICS wajen bukatar sake fasalin tsarin mulki da tsarin tattalin arzikin duniya.”

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu dariya bayan Trump ya ki gayyatar shi taron shugabannin Afrika

Dakin taron BRICS na 2025 a Brazil
Dakin taron BRICS na 2025 a Brazil. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin gyara tsarin kiwon lafiya da rage gibin da ke tsakanin kasashe masu arziki da masu tasowa.

Maganar Bola Tinubu kan sauyin yanayi

Shugaba Tinubu ya nuna damuwa kan matsalar sauyin yanayi da tabarbarewar muhalli wanda ya ce yana shafar ci gaban Afirka.

Ya ce Afirka ba ta da gagarumar rawar da ta taka wajen gurbata yanayi duk da ita ce ke fama da mummunar illar hakan.

Damuwar BRICS kan rikicin duniya

A jawabin da kungiyar BRICS ta fitar bayan taronta na Brazil, ta soki farmaki da aka kai kan Iran, sai dai ba ta ambaci Amurka ko shugabanta kai tsaye ba.

Sararin samaniyar Iran yayin yaki da Isra'ila a watan da ya wuce
Sararin samaniyar Iran yayin yaki da Isra'ila a watan da ya wuce. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton CNBC ya nuna cewa taron ya kuma nuna damuwa kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, amma bai zargi Isra’ila ko Rasha kai tsaye ba.

Maganar Tinubu kan tattali a taron BRICS

Shugaba Tinubu ya ce Najeriya na daukar matakai da dama wajen sauya tsarin tattalin arziki da kare lafiyar jama’a.

Kara karanta wannan

Shiga ADC: Ministan Buhari, Hadi Sirika ya karyata Wike da fadar shugaban kasa

Ya ce Najeriya na kokarin bunkasa amfani da makamashi mai tsafta, da kyautata lafiyar jama’a, da sauya manufofin kiwon lafiya da sauyin yanayi.

Shugaba Tinubu ya ce Najeriya na da cikakken imani da hadin gwiwar kasashe don cimma muradun duniya.

Tinubu tare da tsohuwar ministan kudin Najeriya a yayin taron BRICS a Brazil.
Tinubu tare da tsohuwar ministan kudin Najeriya, Ngozi Iweala a taron BRICS a Brazil. Hoto: @NOIweala
Source: Twitter

Ya kara da cewa wajibi ne a gina duniya da za ta dauki kowa a matsayin uwa daya uba daya, wacce za ta amfanar da kowa da cigaban da ake samu a duniya.

Shugaba Tinubu ya samu rakiyar ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar da ministan kudi, Wale Edun a wannan taro.

An karrama Tinubu a St. Lucia

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sait Lucia kafin wucewa Brazil taron BRICS.

Legit ta rahoto cewa an ba Bola Tinubu lambar yabo mafi girma a kasar St. Lucia saboda gudumawar da ya ke bayarwa.

Shugaban Najeriya ya yi jawabi na musamman a 'yan majalisar kasar, kuma ya mika godiya ta musamman saboda karrama shi da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng