An Kama Ɗan Shekara 25 Ɗauke da Nonon Mace, Ƴan Sanda Sun Yi Ƙarin Bayani
- Rundunar ƴan sandan Anambra ta kama Samuel Eze mai shekaru 25 da nonon mace da aka yanke, yayin wani aikin sintiri a ranar Lahadi
- Ƴan sanda sun kuma ceto direban babbar mota da aka sace, tare da kwato kayayyakin sama da Naira miliyan 9.5 da aka karkatar zuwa Delta
- Haka kuma, rundunar ta kwato motar Toyota Sienna da ake zargin ta sata ce, inda ta yi kira ga mai ita da ya hanzarta zuwa don ya karbi kayansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra – Rundunar ƴan sandan Anambra ta sanar da cewa jami'anta sun kama wani mutum mai shekaru 25 da nonon mace da aka yanke a yankin Awada na jihar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Tochukwu Ikenga, kakakin ƴan sandan jihar, ya ce an kama wanda ake zargin, mai suna Samuel Eze, a ranar 6 ga Yulin 2025.

Source: Facebook
An kama dan shekara 25 da nonon mace
Ikenga ya bayyana cewa an kwace sassan jikin matar daga hannun wanda ake zargin kuma an ajiye nonon a ɗakin ajiye gawarwaki yayin da bincike ke ci gaba, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar Tochukwu Ikenga ta ce:
“Jami'an tsaron hadɗin gwiwa da suka haɗa da ƴan sanda daga ofishin ƴan sanda na Awada da jami’an sa kai na Anambra, sun kama wani wani mutum da ake zargi, Samuel Eze.
"An kama Samuel Eze, mai shekaru 25 ne yayin da jami'an ke sintiri a kan titin Jude Onyekwere, Awada, Obosi a ranar 6 ga Yulin 2025 da ƙarfe 3:30 na yamma."
"An kwato nonon nan take kuma an ajiye shi a ɗakin ajiye gawarwaki don adanawa, yayin da ake yi wa wanda ake zargin tambayoyi don ɗaukar matakan bincike da gurfanarwa."
'Yan sanda sun ceto direba, an kwato kayan sata
A wani samamen na daban, Ikenga ya ce jami'an 'yan sanda sun ceto wani direban babbar mota da aka sace tare da kwato kayayyaki masu darajar sama da Naira miliyan 9.5.
Premium Times ta rahoto kakakin ƴan sandan ya lura cewa an gudanar da samamen ceton ne da ƙarfe 12:45 na rana a ranar 4 ga Yuli, biyo bayan bayanan sirri da aka samu.
Ya ce an kama waɗanda ake zargi su uku, waɗanda aka bayyana sunayensu da: Udegenyi Ugochukwu; Anayochukwu Okonkwo; da Good Odigili.
Sanarwar ta ce:
“Waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun karkatar da wata babbar mota ɗauke da garin Custard wanda direban ke hanyar kai kayan Asaba, jihar Delta.
“Sun ɗaure direban a cikin daji kuma sun karkatar da kayan zuwa Enugwu-Ukwu.”

Source: Original
An kwato motar sata a ƙauyen Obosi
Ikenga ya lura cewa rundunar ta kuma kwato wata motar sata, kirar Toyota Sienna, mai lambar rajista 736 JP, tare da rubutun ‘kungiyar akawun jihar Delta' a ranar 5 ga Yuli yayin da ake sintiri a kan titin Okpuno-Umuota a ƙauyen Obosi.
Ya buƙaci duk wanda ke da hujjar mallakar wannan mota da ya ziyarci hedkwatar rundunar don tantancewa da kuma yiwuwar karɓar ta.
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da haɗin gwiwar sintiri na tsaro don yaƙar rashin tsaro a jihar Anambra.
Jami'an DSS sun harbe dan sanda a Anambra
A wani labarin, mun ruwairo cewa, wani dan sanda mai mukamin Sufeto, Bello Abdulahi, ya rasa ransa a Uli, jihar Anambra, bayan harbin da aka yi masa yayin aikin duba motoci.
Rahotanni sun ce jami’an DSS ne suka harbe shi, sakamakon takaddama da ta taso lokacin da aka tsayar da motarsu.
Hukumar DSS ta fara bincike kan lamarin, yayin da ake ƙara jan hankali kan bukatar kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro don kaucewa irin wannan matsala a gaba.
Asali: Legit.ng


