Najeriya Ta Yi Rashi, Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Ya Rasu
- Tsohon shugaban majalisar wakilai a shekarar 1992, Agunwa Anakwe ya rasu a ranar Asabar da ta gabata
- An tabbatar da mutuwarsa ne ta bakin kwamishinan bayanai na jihar Anambra, Law Mefor, a wata hira ta waya
- Tsohon gwamnan Anambra, Chris Ngige, ya bayyana marigayin a matsayin abokin fafutuka da ya tsaya masa a siyasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra - Najeriya ta shiga jimami bayan tabbatar da rasuwar tsohon shugaban majalisar wakilai a zamanin gwamnatin riko ta Ernest Shonekan a 1992, Agunwa Anakwe.
Kwamishinan yada labarai na jihar Anambra, Law Mefor, ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta waya da aka yi da shi a ranar Litinin.

Source: Facebook
Anakwe, wanda ya shugabanci majalisar a lokacin da yake da shekaru 36, ya rasu ne a ranar Asabar kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Anakwe ya rasu bayan fama da rashin lafiya
Ko da yake ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba a hukumance, wasu rahotanni sun nuna cewa marigayin ya dade yana fama da wata cuta kafin ya rigamu gidan gaskiya.
A cewar tsohon ministan kwadago kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Chris Ngige, Anakwe ya kasance mutum mai basira da natsuwa.
Ngige ya ce marigayin ya tafiyar da majalisar da hikima da fahimta kafin sojoji su kwace mulki a shekarar 1993 bayan soke zaben MKO Abiola.
Arise News ta wallafa cewa Chiris Ngige ya ce:
“Ya jagoranci majalisar ne da natsuwa da kwarewa, lamarin da ya sa majalisar wakilai ta fi ta dattawa kwanciyar hankali kafin juyin mulkin Janar Sani Abacha.”
'Anakwe ya kasance sahihin aboki' - Ngige
Ngige ya bayyana marigayin a matsayin abokin siyasa da ya tsaya masa a lokacin mulkinsa, inda suka hada gwiwa wajen samun nasara a jihar Anambra.
Ya ce:
“A matsayinsa na tsohon kakakin majalisa, ya tsaya da ni lokacin da nake gwamna wajen yakar ’yan siyasar da suka yi wa jihar katsalandan,
Musamman a zamanin Mbadinuju da aka samu matsaloli da albashi da makarantun gwamnati.”
Ngige ya ce ya ziyarci marigayin a karshen Maris da ta wuce, lokacin da ya ji ana shirin masa tiyata, inda suka yi dariya da tattaunawa ba tare da sanin mutuwa na daf da zuwa masa ba.

Source: Facebook
Tasirin rayuwar a Anakwe siyasar Najeriya
Tsohon gwamnan ya bayyana mutuwar Anakwe a matsayin babban gibi a siyasar Najeriya, la’akari da karancin ’yan siyasa masu gaskiya da rikon amana a kasar.
Ngige ya ce:
“Mutuwarsa ta bar babban gibi, domin Anakwe na cikin ’yan siyasa kalilan da ke da gaskiya da tsayawa a kan akida a siyasar kasar nan.”
Marigayin ya rasu yana da shekaru 68, kuma ana kiran shi da lakabin “Ide Anaocha,” yana daga cikin fitattun ’yan siyasa daga jihar Anambra.
An yi jimamin rasuwar Jibril Aminu
A wani rahoton, kun ji cewa an yi jimamin rasuwar Farfesa Jibrin Aminu da ya riga mu gidan gaskiya a kwanakin baya.
Farfesa Jibrin Aminu na cikin manyan Arewa da suka taka rawa wajen rike manyan mukaman gwamnati da siyasa.
Shugaban kasa Bola Tinubu, Atiku Abubakar, gwamnoni da sauran manyan kasa sun yi ta'aziyyar rasuwar tsohon ministan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


