Bincike Ya Gano Gaskiyar Zancen Rasuwar Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari

Bincike Ya Gano Gaskiyar Zancen Rasuwar Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari

  • Wasu ‘yan Najeriya sun fara yada cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu kuma har an gudanar da jana'izarsa
  • Lamarin ya biyo bayan rahoton rashin lafiyar tsohon shugaban kasa, har ta kai shi kwanciya a daki na musamman, wato ICU
  • A bidiyon da aka wallafa na jana'izar Buhari, an hango manyan 'yan siyasa da suka hada da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Wasu daga cikin ‘yan Najeriya masu amfani da shafukan sada zumunta sun fara yada jita-jitar cewa ana fargabar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rasu.

Wannan radi-radi na zuwa ne kwanaki kadan bayan labarin da ke cewa tsohon shugaban ya sha fama da rashin lafiya mai tsanani a birnin Landan.

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
An fara yada 'rasuwar' tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Twitter

Wani mai amfani da shafin X mai suna @USBiafraFirst ya wallafa bidiyo mai tsawon dakika 52 dauke da taken: “An bayyana rasuwar Muhammad Buhari.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon, an hada wani hoton jana’iza da hotuna da kuma faifan bidiyo na tsohon shugaban kasa Buhari, inda aka rubuta “RIP” a kansu.

Yadda aka nuna ‘jana’izar Muhammadu Buhari’

Wani bincike da cibiyar binciken kwakwaf ta Foundation for Investigative Journalism (FIJ) ta gudanar ya nuna cewa mutane da dama sun fara mayar da martani kan yadda aka nuna jana’izar Buhari.

Sai dai binciken ya gano cewa bidiyon da ake yadawa ba na Buhari bane, an dauko shi ne daga wata jana'iza da aka gudanar tun a watan Maris.

Wasu n ayada cewa tsohon shugaba Buhari ya kwanta dama
An karyata labarin jana'izar Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Getty Images

Bidiyon na nuni da jana’izar Hajiya Safara’u Umaru Radda, mahaifiyar gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, da aka yi a garin su Raɗɗa.

Haka nan, majiyoyi da dama daga rahotannin kafafen labarai da wallafa a Facebook, X da Instagram sun tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya

An karyata zancen jana’izar Buhari

Daya daga cikin wadanda suka wallafa bidiyon a wancan lokaci shi ne Abdulrahman Abdulbasir, wanda ke cikin tawagar yada labarai ta gwamna Radda.

A rubutun da ya wallafa ranar 23 ga Maris, ya bayyana cewa:

“Jana’izar marigayiya Hajiya Safara’u Umaru Radda, mahaifiyar gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, da aka gudanar yau a garinsu Raɗɗa. Gwamnan Kano Yusuf Abba da takwaransa na Jigawa Umar Sulaiman Namadi sun halarta.”

Bincike ya tabbatar cewa bidiyon ya riga ya yadu tun a watan Maris a wasu kafafen sada zumunta, kuma ba shi da alaka da Buhari.

Tasirin labaran karya ga 'yan Najeriya

Yaduwar jita-jita da labaran ƙarya a Najeriya na ƙara dagula al’umma da rage amincewa da gaskiyar labarai.

Wannan matsala ta fi ƙamari a lokacin da ake fama da rashin ciakken bayani kai tsaye daga hukumomi ko shahararrun mutane.

A dalilin wannan yanayi, bata-garin mutane sukan cika gurbin rashin cikakken bayani da hasashe da labaran karya da suka samo daga dandalin sada zumunta.

Kara karanta wannan

"Ba a kama shugaban ADC yana cusa daloli a aljihu ba," Dalung ya wanke ƴan APC tas

An taba cewa Buhari ya mutu

Misali, a lokacin mulkinsa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fuskanci jita-jitar mutuwa, musamman bayan ya shafe watanni a birnin Landan yana jinya a shekarar 2017.

A wancan lokaci, wasu sun yi ikirarin cewa Buhari ya mutu kuma an maye gurbinsa da wani mai kama da shi daga Sudan mai suna Jubril.

Wannan jita-jita ta ci gaba da yaduwa har ta dauki hankalin duniya, duk da cewa babu wata shaida ta gaskiya da ta tabbatar da hakan.

Halin da ake ciki yanzu, inda ake yada cewa Buhari ya mutu kuma an yi jana'izarsa, ya sake nuna irin hatsarin da ke tattare da yaduwar labaran karya.

Wannan na iya haifar da tashin hankali, ɓacin rai, da rashin kwanciyar hankali a tsakanin jama’a, musamman idan wadanda suka mutu sun daɗe suna jan hankalin jama’a.

Muhammadu Buhari ya sha jinya

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na fama da rashin lafiya mai tsanani a wani asibiti da ke ƙasar Birtaniya.

Kara karanta wannan

'Barci ba naka ba ne,' Malamin addini ya zaburar da Tinubu kan haɗakar ADC

Labarin ya bayyana cewa Buhari na kwance ne a dakin kulawa da marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta musamman (ICU) a lokacin da aka fara kwantar da shi.

An ruwaito cewa tsohon shugaban ya yi rashin lafiyar ne a lokacin da ake duba lafiyarsa a kasa, amma yana ci gabda da samun sauki sannu a hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng