Tashin Hankali: Sabon Rikici Ya Barke a Adamawa, An Fara Cinnawa Gidaje Wuta
- Sabon rikici ya ɓarke a kauyukan Lafiya da Boshikiri na jihar Adamawa, inda aka ƙone gidajen wasu makera tare da asarar dukiya mai yawa
- Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta tabbatar da cewa gidajen da aka ƙone sun haɗa da na Ododumga Kenneth da Nura Haruna
- Kwamishinan ‘yan sanda ya yi gargaɗi ga masu tayar da tarzoma da neman haɗin kai daga jama’a don hana cigaban rikici da kama masu laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Sabon tashin hankali ya ɓarke a jihar Adamawa, inda rahotanni suka tabbatar da hare-hare a kauyukan Lafiya da Boshikiri da ke ƙananan hukumomin Lamurde da Guyuk.
Rikicin, wanda ya zama ruwan dare a lokutan damina tsakanin mutanen yankin, ya haifar da asarar dukiya mai yawa a ranar Laraba.

Source: Twitter
An kona gidaje 2 a rikicin jihar Adamawa

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, su buɗe wuta ana tsakiyar Sallah a jihar Sakkwato
Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta fitar da sanarwa a ranar Alhamis a shafinta na X, inda ta bayyana cewa an “ƙona gidaje da gangan” ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, wasu da ba a san ko su wane ba sun banka wa gidajen wuta a kauyen Lafiya (karamar hukumar Lamurde) da Boshikiri (karamar hukumar Guyuk).
An tabbatar da cewa gidajen da aka cinnawa wuta sun haɗa da na Mrs. Ododumga Kenneth a Lafiya da kuma na Mr. Nura Haruna a Boshikiri, kuma sun ƙone ƙurmus.
'Yan sanda sun gargadi masu tayar da tarzoma
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Dankombo Morris, ya bayar da umarnin fara bincike na musamman tare da tura jami'an tsaro zuwa yankunan domin hana cigaban rikicin da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.
Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama da hannu wajen tayar da tarzoma ko aikata wani laifi, za a hukunta shi dai-dai da tanadin doka.
Rundunar ta bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su haɗa kai da ‘yan sanda, tare da bayar da rahoto kan duk wata alama ta barazana ko motsin mutane da ba a saba da shi ba.

Source: Original
Sanarwar 'yan sanda kan rikicin Adamawa
Ga abin da sanarwar ta ƙunsa:
“Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa na Allah wadai da abubuwan da suka faru a ranar 2 ga Yuli, 2025, inda wasu da ba a san ko su wane ba suka ƙona gidajen makera a Lafiya (Lamurde) da Boshikiri (Guyuk).
“Gidajen da aka ƙona sun kasance mallakin Mrs. Ododumga Kenneth da Mr. Nura Haruna ne.
“Kwamishinan ‘yan sanda CP Dankombo Morris, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na sirri da kuma tura jami’an tsaro nan take domin hana cigaban rikici da kama masu hannu.
“Kwamishinan ya sake nanata cewa duk wanda aka kama da laifi za a hukunta shi ba tare da wani rangwame ba.
“Rundunar na roƙon jama’a da su kwantar da hankali, su bada haɗin kai da su kuma rika bayar da rahoto cikin gaggawa idan sun ga wani motsi ko ayyuka da ba su yarda da su ba.”

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Fada ya barke tsakanin wasu 'yan gida 1 a Filato, an yi kisan kai
An kona gidaje, rumbunan abinci a Taraba
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu da ake zargin 'yan Jukun ne sun kai hari garin Dekeh da ke kan hanyar Wukari–Kente, inda suka ƙone gidaje 15.
Wannan farmakin da aka kai da misalin ƙarfe 1:00 na dare ya sake tayar da hankalin al’umomin Tiv da Jukun, waɗanda ke fama da rikice-rikicen filaye a jihar Taraba.
Rundunar ‘yan sanda da sojoji sun yi gaggawar kai dauki, an ceto wanda aka harba, sannan aka fara bincike da zaman sulhu don hana ci gaba da rikici.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
