Ana Batun ADC, Tinubu Ya Fadi yadda Ya Samu Najeriya a Wargaje bayan Mulkin Buhari
- Shugaba Bola Tinubu ya ce ya gaji Najeriya tana dab da durƙushewa amma ya ɗauki matakai na farfado da tattalin arziki
- Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan Najeriya mazauna ƙasar Saint Lucia a yankin Caribbean
- Bola Tinubu ya ce gwamnati na aiki kan manufofi masu ɗorewa da za su jawo masu zuba jari da inganta rayuwar jama’a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saint Lucia - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce mulkinsa ya samu ƙasar a lokacin da tattalin arzikinta ke dab da rushewa, amma yanzu an fara ganin sauyi.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakan gyara da ke farfaɗo da amincewar masu zuba jari da sake daidaita al’amuran ƙasa.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa shugaban ya bayyana haka ne a wani taron ganawa da ‘yan Najeriya da ke zaune a ƙasar Saint Lucia da ke yankin Caribbean.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya bayyanawa mahalarta taron irin ƙalubalen da ya samu da kuma matakan da yake ɗauka don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.
Bola Tinubu ya ce ya hana Najeriya rugujewa
Shugaba Tinubu ya ce bayan shigarsa ofis, ya fahimci cewa Najeriya na dab da durƙushewa, amma gwamnatinsa ta ƙaddamar da gyare-gyare domin hana hakan.
A cewar shugaban kasar, karya darajar Naira da cire tallafin man fetur na cikin matakan da ya dauka a karon farko.
Ya kuma ce duk da ƙarancin kuɗin shiga da talakawan Najeriya ke fuskanta, gwamnatinsa na aiwatar da manufofi masu ɗorewa domin ƙarfafa ci gaba da bunƙasa tattalin arziki.
Alkawarin Tinubu ga 'yan Najeriya a ketare
A yayin taron, Tinubu ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya mazauna ƙasar cewa gwamnati ba za ta manta da su ba.
Shugaban ya buƙace su da su dage da aiki da gaskiya a duk inda suke, domin gwamnati za ta ba su goyon baya.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi wa Tinubu dariya bayan Trump ya ki gayyatar shi taron shugabannin Afrika
The Nation ta wallafa cewa Tinubu ya ce:
“’Yan Najeriya da ke ƙasashen waje, ba za mu manta da ku ba. Amma ya kamata ku dage, mu kuma za mu taimaka muku ku samu nasara.”
Taron ya samu halartar shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, wadda ta yaba da irin gudunmuwar da ‘yan ƙasar ke bayarwa a Saint Lucia.

Source: Twitter
'Yan Najeriya sun yi godiya ga Bola Tinubu
Wata likita, Dr. Olugbemisola Ogunlusi, da ta bar Najeriya zuwa Saint Lucia shekaru kusan 20 da suka gabata, ta yaba da zuwan shugaban Najeriya kasar.
Taron ya ba wa shugaba Tinubu dama ya saurari batutuwan da ke damun ‘yan Najeriya a ƙetare tare da tabbatar musu da cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai don farfaɗo da ƙasa.
Legit ta tattauna da Abbas Hassan
Wani matashi a jihar Kano, Abbas Hassan ya bayyanawa Legit cewa shi bai aminta da kalaman da Bola Tinubu ya yi ba.
Abbas ya ce:
"Kamar yana son kaucewa nauyin da ya ke kansa ne. Ya san halin da kasar ke ciki ya nemi mulkin. Mu da zai mayar da mu baya ma da ya fi mana."
An karrama Bola Tinubu a St. Lucia
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya samu lambar girma a kasar Lucia.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa lambar yabon da aka ba Bola Tinubu ita ce mafi girma a kasar.
Shugaba Bola Tinubu ya yi godiya bisa karrama shi da aka yi tare da bayyana cewa Najeriya za ta ciga da hada kai da Lucia.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

