Saukin da Ƴan Najeriya Ke Murnar Samu a Farashin Fetur Ya Gamu da Cikas daga Ƴan Kasuwa

Saukin da Ƴan Najeriya Ke Murnar Samu a Farashin Fetur Ya Gamu da Cikas daga Ƴan Kasuwa

  • Ƴan kasuwa sun ki sauke farashin man fetur a gidajen ma duk da matatar Ɗangote ta rage N40 a kowace ƙitar da take sayar masu
  • A cewarsu, ba za su iya sauke farashi ba a yanzu saboda suna da tsohon kaya wanda suka saya da tsada kafin samun sauƙi
  • Shugaban ƙungiyar PETRON na ƙasa ya ce ƴan kasuwa za su tafka asara idan suka rage farashin kowace lita a yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Duk da matatar Ɗangote ta sauke farashin litar fetur daga N880 zuwa N840, ƴan kasuwa sun ƙi ragewa a gidajen mai ballantana jama'a su amfana.

Ƴan kasuwar sun bayyana cewa ba za su rage farashin fetur ba har sai sun sayar da wanda ke hannunsu saboda sun sayo shi a tsohon farashi.

Farashin man fetur bai ragu ba a gidajen mai.
Yan kasuwa sun ƙi sauke farashin man fetur duk da rangwamen da matatar Ɗangote ta yi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suka tattauna da Punch a ranar Talata sun bayyana cewa ba za su iya rage farashin mai ba sai wanda suka sayo a N900 kowace lita ya ƙare.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan kwallon kafa 10 da suka mutu a hadari suna cikin tashe a duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Ɗangote ta rage N40 a kowace lita

A daren Litinin, matatar Dangote ta rage farashin sayar da fetur ga ƴan kasuwa a rumbun ajiya daga N880 zuwa N840 kowanne lita.

Kakakin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa matakin zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Yuni, 2025.

A ranar Talata, wasu rumbunan ajiya da masu shigo da fetur sun daidaita farashinsu da sabon tsarin, saboda saukar danyen mai bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran.

Daga N920, rumbuna da dama da ke sayar da fetur ga ƴan kasuwa sun saukar da farashin kowace lita zuwa N845.

Duk da cewa matatar Dangote ta rage farashi da N40, ‘yan Najeriya sun sa ran cewa gidajen mai za su sauke na su amma bincike ya nuna farashin bai sauka ba har yanzu.

Ƴan kasuwa sun ƙi rage kudin litar fetur

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, su buɗe wuta ana tsakiyar Sallah a jihar Sakkwato

Abokan huldar Dangote kamar kamfanin mai na MRS, Heyden da AP ba su sauya farashi ba duk da rangwamen da aka samu, hakan ya sa wasu gidajen man ba su rage ba.

Rahotanni sun nuna cewa a jiya Talata, an sayar da kowace litar fetur tsakanin N920 zuwa N935 a jihar Ogun da sauran yankin Kudu maso Yamma.

Masana sun bayyana cewa ya kamata gidajen mai su rage farashinsu bayan Dangote ya cire masu N40 daga yadda yake sayar masu kowace lita.

Saukin fetur da aka samu daga matatar Ɗangote ya gamu da cikas.
Yan kasuwa sun ce har yanzu suna da tsohon kaya da suka saya kan N920 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Me yasa ƴan kasuwa ba su rage farashin fetur ba?

Amma shugaban ƙungiyar masu gidajen mai na ƙasa (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya ce ba su rage farashin ba ne saboda suna da tsohon kaya da suka saya da tsada.

Gillis-Harry ya ce:

“Ta yaya farashin zai sauka? Idan kai ɗan kasuwa ne, ka siya fetur a N920 kuma sai farashi ya sauka zuwa N840, me zaka yi?
"Idan ka ɗauki N80 ka nunka ta sau lita 45,000, nawa za ka samu? Za a yi asara da yawa, hakan ba zai yiwu ba.”

Legit Hausa ta samu jin ta bakin Muhammadu Bello, wani manomi wanda ke amfani da fetur a harkokinsa na yau da kullum, ya ce ya daina tunanin samun sauƙi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

ADC: An bayyana wanda zai jagoranci haɗakar su Atiku zuwa fadar shugaban ƙasa a 2027

A cewarsa, yanzu yana harkokinsa ne daidai ƙarfinsa, amma ya daina tsaya wa jiran wai mai zai sauka a gidajen mai.

Muhammad ya ce:

"Yanzu sai dai mu ce Allah ya kawo mana sauƙi, amma ba zancen ragin N40 ake ba kwanan nan, jiya na je sayen fetur, ka san nawa na sayo lita? N950.
"To taya zaka tsaya jiran wai mai ya sauka, kuma abin haushin idan ka bibiya za ga can saman sun rage kamar yadda suka faɗa, amma waɗanda ke tsakaninmu da su ne matsalar."

Matatar Ɗangote ta ɓullo da tsarin jigila

A baya, kun ji cewa matatar man Ɗangote ta ɓullo da wani tsari na rabawa ƴan kasuwa feturin da suka saya har gidajen mansu kyauta.

Ta bayyana cewa tsarin zai bai wa masu gidajen mai, kamfanonin sadarwa damar samun kayan da suka saya cikin sauki.

Matatar na shirin amfani da manyan motoci 4,000 masu amfani da iskar CNG domin rage dogaro da direbobin haya da kuma inganta tsarin jigilar mai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262