An Wallafa Sunayen Mutum 14 da aka Cafke Suna Shirin kai Hari Jihar Benue
- Jami’an tsaro sun kama mutum 14 da ake zargi da kasancewa mambobin kungiyar ta’addanci karkashin jagoransu mai suna Konyo
- Bayanai da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an kama su ne yayin samamen hadin gwiwa a hanyar Katsina-Ala zuwa Takum
- Rahotanni sun tabbatar da cewa duk wanda aka kama ’yan asalin garin Gbise ne, kuma suna da hannu a garkuwa da mutane a yankin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Rundunar hadin gwiwa ta kama mutum 14 da ake zargi da kasancewa mambobin gungun ‘yan bindiga da ke karkashin jagorancin jagoran ‘yan ta’adda mai suna Konyo.
An kama mutanen ne a wani sintiri da aka gudanar a ranar Litinin a hanyar Katsina-Ala zuwa Takum, biyo bayan rahoton leƙen asiri da ya nuna cewa ana shirin kai hari a garin Tor-Donga.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa mutanen da aka kama na cikin masu haddasa rikice-rikice, garkuwa da mutane da kuma kai farmaki a wasu yankuna da ke kewaye da Gbise.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen mutanen da aka kama a Benue
An bayyana sunayen waɗanda aka tabbatar da kasancewa cikin gungun Konyo da suka haɗa da Awuhe Terungwa, Asawa Terseer, Terkura Audu, Terseer Gusa, Sesugh Terver da Dengba Tersugh Benjamin.
Sauran sun haɗa da Goji Abraham, Joshua Ioraenyi, Chia Fanen, Mson Iorfa, Terhemen Yanmeer, Yerfa Iorchir, Viashima Ngutor da Vendaga Anthony – duk ’yan asalin Gbise ne.
An ce jami’an tsaro sun kama su ne bayan an gano wasu na yawo a bakin hanya, kafin daga bisani a tsananta bincike kuma a kamo sauran a dajin kusa da wurin.
Jami’an tsaro sun ƙarfafa sintiri a Benue
Rahoton ya bayyana cewa samamen ya kasance cikin nasara ne sakamakon samun bayanin leƙen asiri da ya taimaka wa wajen kai farmakin da ya dakile harin da ake shirin kaiwa.
Rundunar soji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun ƙara sanya idanu a yankin domin hana faruwar wani sabon tashin hankali.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ko akwai wasu da suka tsere da kuma bankado shirin 'yan ƙungiyar Konyo a yankin.

Source: Facebook
Ana ƙara sanya ido kan yaran dan ta'adda Konyo
Gungun Konyo na daga cikin mafiya haɗari a yankin Arewa ta Tsakiya, inda aka dade ana zargin su da aikata laifuffuka irin su satar mutane da farmaki da kuma kashe fararen hula.
Jami’an tsaro sun sha bayyana cewa za su ci gaba da aiki kafada da kafada domin dakile ayyukan masu tada hankali da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Benue.
An kashe 'yan Kano a jihar Benue
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane da ba a gano su waye ba sun kashe matafiya 'yan asalin jihar Kano a Benue.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda aka kashe din 'yaran malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil ne.
Gwamnatin Kano, karkashin Abba Kabir Yusuf ta yi Allah wadai da kisan tare da kira a hukunta wanda suka yi kisan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

