Jama'atul Nasril Islam Ta Yi Magana kan Karuwar Kashe Kashe, Ta'adanci da Farfadowar Boko Haram
- Kungiyar Jama'atul Nasril Islam ta nuna damuwa kan yawaitar sace-sace, kashe-kashe, da dawowar Boko Haram
- JNI a karkashin Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III ta ce lamarin rashin tsaro na kara ta'azzara
- Ta ce 'yan Najeriya sun fusata, kuma sun fara fitar da rai da cewa gwamnatin tarayya za ta iya tsare dukiya da rayukansu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ta ce akwai damuwa a kan lamarin tsaron kasa.
JNI ta koka kan hauhawar rikice-rikicen ƙabilanci da sake fitowar mayaƙan Boko Haram a wasu sassa na ƙasar nan.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar ta fitar da wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren ta na ƙasa, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, inda ta bayyana fargaba kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
JNI ta caccaki gwamnatin Najeriya
JNI ta zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen ɗaukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalolin tsaro a ƙasar.
Kungiyar ta nuna matuƙar mamaki kan yadda jami’an tsaro ke kasa dakile hare-haren da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda ke kaiwa a kan al’umma.
Ta bayyana rashin jin daɗi kan yadda babu wani cigaba a bincike da hukunta wadanda suka aikata kisan baki da baƙi na bikin aure da aka kashe a jihar Filato.

Source: Facebook
JNI ta kuma jaddada cewa ‘yan Najeriya sun fara gajiya da halin da ake ciki, kuma suna rasa kwarin gwiwa a kan yiwuwar gwamnati na kare su daga barazana.
Kiran kungiyar JNI ga gwamnatin tarayya
JNI ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakan da suka dace domin hana rikice-rikicen da ke yawaita a sassan Najeriya kafin su kazanta fiye da kima.

Kara karanta wannan
NAHCON ta samu tsaiko a jigilar alhazan Najeriya zuwa gida, za su ƙara zama a Saudiyya
A cewar JNI:
“Ya kamata gwamnati ta kasance mai saurin ɗaukar mataki kan harkokin tsaro. Yawan faruwar rikice-rikice, ciki har da sace mutane, kashe-kashe, sake bayyanar ta’addanci daga Boko Haram da rikicin ƙabilanci a sassa daban-daban na Najeriya abin damuwa ne ƙwarai."
“Al’umma na kara fusata musamman kan kisan gillar da aka yi a Mangu. An san wuraren da rikice-rikicen ke faruwa amma babu abin da ake yi. Ya kamata a tura jami’an tsaro cikin tsari zuwa irin waɗannan wurare.”
“Hedikwatar ƙasa ta Jama’atu Nasril Islam, bayan yin nazari mai zurfi da kuma bibiyar abubuwan da suka faru, ta bayyana cewa harin da wasu matasa Kiristoci suka kai wa Musulmi a jihar Filato alamar rashin imani ne da ɗabi’ar dabbanci.”
JNI ta shawarci jami'an tsaro
A baya, mun wallafa cewa Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bayyana matuƙar takaici a kan yadda rayuka ke ci gaba da salwanta a jihar Binuwai.
JNI ta bayyana cewa ci gaba da yin shiru a kan kashe-kashen da ake ta fama da su a jihar ba zai haifar da alheri ba ga zaman lafiyar Najeriya baki ɗaya.
Ta ce ya kamata jami'an tsaron kasar nan su farka, su rika kokarin dakile hare-hare kafin faruwarsu, domin ta haka ne kawai za a rage asarar rayuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
