Kungiyar Jama'atu Nasril Islam tayi kira da a zauna lafiya kan batun adan kabilanci
- Shugaban Jama'atul Nasril Islam JNI yace a zauna lafiya kada a dauki fansa
- Kiran Ya biyo bayan Hare-heren Kungiyar Masu Fafutakar kafa Kasar Biafra IPOB tayi akan Yan'arewa mazauna kudancin kasarnan
- Harin dai yayi sanadiyar rasa rayuka da ma dukiyoyin mutan arewa mazauna yankunan kudun, kuma mafi yawancinsu yan Arewa ne
Shugaban Jama'atul Nasril Islam JNI yayi kira ga matasan Yankin Arewacin najeriyya da Suyi hakuri kada su tada zaune tsaye.
Biyo bayan harin da aka kaiwa 'yan arewa a kudu maso gabashin Najjeriya ya sa shugabannin arewa musamman na Jama'atul Nasril Islam suke ta kiran jama'arsu kada su dauki fansa kan yan kudu dake zaune a arewa.
Fargabar daukan fansa ta sa shugabanni a duk arewacin Najeriya na ta kiran al'umma kada a dauki matakin fansa a rewacin kasar.
Kungiyar Musulmin Najeriya ta Jama'atul Nasril Islam, JNI, na cewa ya zama wajibi a kira al'umma kada wanda ya dauki fansa.
Sakataren kungiyar ta JNI Dr Kari Aliyu Abubakar shi ya yiwa manema labarai karin haske. Yana mai cewa a matsayinsu na shugabannin addini suna kira a kai hankali nesa. Sun yi anfani da masallatai sun kira a kan zaman lafiya, a kwantar da hankulan mutane musamman matasa tunda gwamnati ta ce za ta dauki matakai.
DUBA WANNAN: Har yanzu Najeriya da man fetur ta dogara, sabon bincike ya nuna
Ita ma kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya ta ce ta gamsu cewa an fara samun zaman lumana a kudancin kasar. Ta kira doka ta yi aikinta akan duk wadanda suka tada hayaniya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng