Sarki a Legas Ya Tube Rawanin Hakimai 6 kan Halartar Taron Jam'iyyar LP
- Sarkin Ijora, Oba AbdulFatai Oyegbemi, ya tuɓe rawanin hakimai shida saboda halartar taron jam'iyyar LP ba tare da izinin sa ba
- Sarkin ya kira hakiman zuwa fadarsa, inda ya bayyana masu takaicinsa kan abin da suka aikata wanda ya ce ya karya dokokin masarautar
- A hannu daya, Sarki AbdulFatai Oyegbemi ya sha alwashin ci gaba da ba gwamnatin Legas goyon baya wajen gina al'ummar masarautarsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Sarkin Ijora da Masarautar Iganmu, Oba AbdulFatai Oyegbemi, ya tuɓe rawanin hakimai shida saboda halartar taron jam'iyyar LP a yankin Apapa na jihar Legas.
Sarki AbdulFatai ya bayyana cewa hakiman sun halarci taron siyasar ba tare da izinin sa ba, kuma sun karya dokokin fada ta hanyar nuna cewa shi ne ya tura su wakilci a wurin taron.

Source: UGC
Sarki a Legas ya tube rawanin hakimai 6
Jaridar The Punch ta rahoto cewa wadanda dakatarwar ta shafa sun hada da:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Chief Lateef Ojora (Bale Alaba Oro)
- Chief Saliu Biliamin (Bale Alafia Dodoro)
- Chief Taiwo Hassan (Bale Oke Ira)
- Chief Idris Ojora (Bale Abule Kere)
- Chief Hakeem Oseni (Bale Mosafejo Amukoko)
- Chief Sule Balogun (Balogun na Abule Kere)
Sarki AbdulFatai ya kira hakimai fadarsa
Wannan dakatarwar ta biyo bayan wani taron fada da aka gudanar a ranar Litinin, inda Sarki AbdulFatai ya nuna cewa ba zai lamunci ayyukan hakiman ba.
A cikin wata sanarwa da jaridar ta gani ranar Talata, masarautar ta bayyana cewa:
"Bayan ganin wadanda hakimai a wajen taron siyasa, wanda suka halarta ba tare da yawunsa ba, Sarkin Ojora ya kira hakimai, Balogun, da 'yan majalisun Ojora zuwa fadarsa domin sanin dalilin abin da ya faru.
"Bayan sauraron su, cikin ikonsa na Sarki, Oba AbdulFatai ya nuna takaici kan abin da suka aikata, kuma ya shaida wa masu sarautar cewa sun saba ka'idar ayyukansu.

Kara karanta wannan
"Ba dan Allah ba ne," An gano abin da ke tilastawa gwamnonin PDP sauya sheƙa zuwa APC
"Ya sake nanata cewa babu wani hakimi da zai yanke shawara ko ya yi aiki a madadinsa ba tare da izinin sa ba, domin dukkaninsu suna wakiltarsa ne da kuma tabbatar da al'adun ƙasar."

Source: Facebook
Sarki AbdulFatai ya tunatar da hakimai aikinsu
Sanarwar ta kara da cewa:
"Matakin tuɓe rawanin hakiman shida ya nuna jajircewar Sarki AbdulFatai wajen kiyaye tsari da daidaito a cikin sha'anin mulkinsa.
"A yayin wannan taron, sarkin ya kuma yi amfani da damar ya yaba wa ci gaban da gwamnati mai ci ke yi a ƙasar Ojora, yana mai bayyana aniyarsa ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin yayin da take inganta al'ummar masarautar."
Sarkin na Legas, ya kuma tabbatar da mahimmancin rarrabewa da kuma kiyaye iyaka a sha'anin gudanar da sarautar gargajiya da kuma shiga harkokin siyasa.
Oba AbdulFatai Oyegbemi, ya kuma tunatar da dukkanin masu sarautu ayyukan da suka rataya a wuyansu yayin da suke hidima a ƙarƙashin masarautar Ojora mai daraja.
Masarautar Katsina ta tube rawanin hakimi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, masarautar Katsina ta sauke Makaman Katsina, Hakimin Bakori, Idris Sule Idris, bisa zargin da ake yi masa dn hannu a ayyukan ta'addanci.
An dauki matakin ne bayan kwamitin bincike da gwamnatin jihar ta kafa ya gano cewa hakimin na da laifi, sakamakon korafe-korafen da mazauna yankinsa suka shigar.
A baya, gwamnatin Katsina ta sauke Sarkin Pawan Katsina, Hakimin Kankara, Yusuf Lawal, shi ma bisa zargin alaka da miyagun da ke addabar yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

