'An Firgita Su,' Mazauna Zamfara Sun Fadi Halin da ake Ciki bayan Kisan Dan Uwan Turji

'An Firgita Su,' Mazauna Zamfara Sun Fadi Halin da ake Ciki bayan Kisan Dan Uwan Turji

  • Fitaccen kwamandan 'yan bindiga kuma dan uwan Bello Turji ya mutu bayan farmakin da matasan sa-kai na Shinkafi suka kai maboyarsu
  • Yanzu haka dai mazauna yankin sun fito domin bayyana jin dadinsu, inda suka ce suna sa ran bana babu wanda zai dora masu harajin noma
  • Sun bayyana fatan gwamnati da matasan za su ci gaba da kai irin wannan farmaki, irinsa na farko mafi muni da aka kaddamar a kan 'yan ta'adda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Jama'a suna ta murna a fadin jihar Zamfara da wasu sassan Arewa maso Yamma bayan tabbacin mutuwar fitaccen kwamandan 'yan bindiga, Kachalla Yellow Danbokolo.

Mutuwar Danbokolo ta biyo bayan mummunan farmaki da rundunar sa-kai ta Shinkafi ta kai a yankin a fafutukar dawo da zaman lafiya yankin.

Kara karanta wannan

Matakan da aka dauka bayan kisan gilla da aka yiwa 'yan Arewa a jihohi 3 na Najeriya

Sojojin Najeriya
Matasan sa kai da jami'an tsaro sun farmanki maboyar Bello Turji Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

AIT ta ruwaito cewa Danbokolo, wanda ake cewa dan uwan Bello Turji ne, ya mutu ne bayan samun raunin bindiga a fafatawar da suka yi da matasan sa-kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe mayakansu Bello Turji

The Nation wallafa cewa ta ce akalla mayakan Danbokolo 173 ne suka rasa rayukansu a harin bazata da mazauna yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan farmaki shi ne irinsa mafi muni da aka taba kai wa 'yan bindiga a yankin.

Duk da cewa ba a tabbatar da rawar da DSS ta taka ba, majiyoyi sun bayyana cewa akwai alamun goyon bayan bayan-fage daga hukumomin leken asiri.

Jami'in sojin Najeryiya
Mazauna Zamfara na murna da kashe dan uwan Bello Turji Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

A yankin Kurya da wasu kauyuka da ke makwabtaka, an wayi gari da shagulgula, ana murna, inda manoma da mazauna ke yankin suka ce za a yi noman bana ba tare da fargaba ba.

Danbokolo, wanda da dama ke bayyana a matsayin jagoran ayyukan ta’addanci, an ce shi ne ke kula da manyan hare-haren yayin da Turji ke zama mai magana da yawun kungiyar.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun harbe dan sanda saboda 'rashin fahimta' a jihar Anambra

Abin da mazauna Zamfara ke cewa

Mazauna Zamfara sun ce ragowar mabiyan Turji yanzu sun rikice, wasu daga cikinsu na neman afuwa yayin da sojoji ke kara matsa lamba.

Wannan ne karon farko da rundunar matasa sa-kai ta kai irin wannan mummunan hari ga sansanin Turji tun bayan da ta’addanci ya dabaibaye yankin.

Mutane sun ce yanzu suna fatan rayuwa a damunar bana cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoron karbar haraji ko kisa ba, suna kuma godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa wannan mataki da aka ba su damar dauka,

Mazauna yankin na ganin cewa mutuwar Danbokolo na iya zama wata sabuwar kafa a yaki da ta’addanci a Arewa maso Yamma, musamman idan aka ci gaba da irin wannan tsari.

An kashe dan bindiga a Zamfara

A baya, kun samu labarin cewa an samu nasarar kashe shahararren dan bindiga, Kachalla Mai Jakka, a wani farmaki da ‘yan sa-kai suka kai a jihar Zamfara bayan ya addabi jama'a.

Kara karanta wannan

Sanata Ningi ya dauki zafi, yana son majalisa ta binciki rashin biyan yan kwangila hakkokinsu

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe shi ne a ranar 25 ga Yuni, 2025, a yankin Mayanchi da ke karamar hukumar Maru ta jihar, kuma ya shahara wajen wallafa kudin fansa a Tiktok.

Wasu majiyoyi sun ce an kashe shi tare da wani abokin aikinsa a wata aranga­ma da ta auku a kusa da kauyen Garaji, da ke kan hanyar Gusau zuwa Sokoto, lamarin da ya yi wa jama'a dadi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng