Ana Shirin Gudanar da Taron NEC, 'Yan Sanda Sun Mamaye Sakatariyar PDP a Abuja
- 'Yan sanda sun mamaye hedikwatar PDP a Abuja yayin da takaddama kan taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) ke ci gaba da ƙaruwa
- An hana mambobi, ma'ikatan jam'iyyar da ƴan jarida shiga harabar sakatariyar, yayin da wasu suka ce an tura 'yan sanda don hana taron
- PDP ta dage cewa taron NEC karo na 100 zai gudana kamar yadda aka tsara, tana mai kira ga 'ya'yanta da su yi watsi da jita-jitar dage shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Litinin ne 'yan sanda ɗauke da makamai suka mamaye Wadata Plaza, hedikwatar jam'iyyar PDP da ke babban birnin tarayya Abuja.
Jami'an sun mamaye hedikwatar ne yayin da takaddama ke ci gaba da ƙaruwa kan taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) na PDP wanda ake sa ran za a gudanar yau.

Source: Twitter
'Yan sanda sun mamaye sakatariyar PDP
'Yan sandan sun kuma hana wani mamba na kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar, Maina Chiroma, shiga harabar sakatariyar, a cewar rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani jami'in jam'iyyar, wanda ya yi magana da wakilin talabijin din a sirrance, ya ce an tura 'yan sanda ne don hana gudanar da taron NEC da aka shirya.
Ko da yake da farko an bar wasu ma'aikatan jam'iyyar su shiga harabar sakatariyar ba tare da wata tangarɗa daga 'yan sanda ba, daga baya kuma aka ga ana korar su.
An kuma umarci ƴan jarida da su bar harabar sakatariyar yayin da aka ga wasu 'yan sanda suna killace titin Dalaba, wanda shine hanyar da ke kaiwa ga Wadata Plaza.
'Ba abin da zai hana taron NEC' - Taofeek
Tun da fari, a ranar Lahadi, PDP ta ce taron kwamitin zartaswa na kasa karo na 100 zai gudana a yau kamar yadda aka tsara a lokacin taron NEC na 99 da aka gudanar makonni da suka gabata.

Kara karanta wannan
'Dan shekara 24 ya yi garkuwa da abokinsa, ya karɓi Naira miliyan 5.3 kuɗin fansa
Jam'iyyar ta shawarci mambobinta da su yi watsi da wata sanarwa da aka yaɗa da ke nuna cewa an dage taron.

Source: UGC
Mataimakin shugaban PDP na kasa, daga Kudu, Ambasada Taofeek Arapaja, ya ba da tabbacin a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin jam'iyyar na X.
Ya bayyana cewa taron NEC zai karɓi sababbin bayanai kan ayyukan kwamitin raba mukamai ga yankuna da kwamitin shirya babban taron kasa.
Ya tuna cewa an yanke shawarar gudanar da taron karo na 100 ne a yayin taron NEC na 99 da aka gudanar a ranar Talata, 27 ga Mayu, 2025.
Karanta cikakkiyar sanarwar a nan kasa:
PDP ta gana da INEC kan taron NEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tawagar PDP ta kai ziyara hedikwatar hukumar INEC domin warware ruɗanin da aka samu game da taron NEC.
Muƙaddashin Shugaban PDP na Kasa, Umar Damagum, ya bayyana cewa sun ziyarci INEC ne domin warware rikicin shugabancin jam'iyyar.
Sai dai, Shugaban INEC, Mahmud Yakubu, ya ce PDP tana yi wa hukumar yawo da hankali game da kujerar sakataren jam'iyyar na ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
