Matakan da aka Dauka bayan Kisan Gilla da aka Yiwa 'Yan Arewa a Jihohi 3 na Najeriya
Kashe-kashen da ake yi wa 'yan Arewa, musamman Hausawa Musulmai, a sassa daban-daban na Najeriya, na ci gaba da jawo damuwa.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jama'a na ganin lamarin na ci gaba da afkuwa kuma babu hukunci, sannan mahukunta na shiru kan batun bayan kwanaki biyu.
Legit ta tattaro bayani kan wasu daga cikin kashe-kashen baya-bayan nan da suka tada hankali a Filato, Edo da Binuwai da halin da ake ciki a yanzu.
1. Yadda aka kashe mutum 13 a Filato
Yawan wadanda suka mutu a harin da wasu mutane suka kai wa fasinjojin da ke hanyarsu zuwa daurin aure a Mangun, karamar hukumar Mangu a jihar Filato, ya karu zuwa mutum 13.

Source: Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ruwaito cewa fasinjojin, wadanda suka hada da maza, mata da yara 32 na tafiya ne cikin wata motar haya mallakin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, daga Basawa a Kaduna zuwa Qua’an Pan a Filato.
Sai dai bayan sun kai yankin Mangun da 8.00 na dare, ranar 20 ga watan Yuni, wasu mugayen mutane suka kai musu hari, inda suka hallaka wasu, suka kona motar, sannan wasu suka jikkata.
Filato: Matakin da aka dauka kan kisan Hausawa
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ya tuntubi gwamnan Filato, Caleb Muftwang, inda ya nemi da a hukunta masu hannu a wannan danyen aiki.
Haka zalika, rundunar ’yan sanda ta jihar Filato ta tabbatar da kama mutane 20, sai dai har yanzu ba a bayyana wani hukunci da aka yanke musu ba.
2. Shiru ake ji bayan hallaka Hausawa a Edo
A jihar Edo kuma, an kashe matasa 16 a wani mummunan hari da wasu matasa suka kai musu a Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa a watan Maris 2025.
A wani al'amari na tsantsar rashin tausayi ko mutunta ran dan Adam, 'yan bijilanti sun shuna wa mazauna garin matafiyan, bisa zargin wai 'yan bindiga.

Source: Twitter
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana bakin ciki bisa wannan kisa, inda ya umarci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su binciko wadanda suka aikata kisan kuma a hukunta su.
Uromi: Abin da aka yi kan kisan Hausawa
Gwamnatin Kano da ta Edo sun sha tattaunawa kan lamarin, inda aka kafa kwamiti karkashin jagorancin mataimakin gwamnan Kano, kwamred AbdulSalam Gwarzo domin duba yiwuwar biyan diyya ga iyalan mamatan.
Sai dai har zuwa yanzu, babu wani bayani ko tabbaci a hukumance kan hukunta wadanda aka kama da hannu a harin, ko kuma iyayen wadanda aka kashe sun samu diyya.
3. Kisan matasan Kano 2 a Binuwai
A wata irin al’amarin da ya kara girgiza al’umma, an kashe wasu matasa biyu 'yan Kano a Makurdi, babban birnin jihar Binuwai, bisa zargin cewa sun yi kama da Fulani.
Wannan kisa ya faru ne yayin da matasan biyu, Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, ke tsaye suna shan shayi a gefen titi.

Source: Facebook
An gudanar da sallar jana’izarsu a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, inda Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, shiga jerin wadanda suka masu sallah.
Kamar sauran kashe-kashen da aka yi, har yanzu babu wani hukunci da aka zartar, kuma ba a ji labarin kama wadanda suka aikata hakan ba.
Martani mazauna Kano kan kisan 'yan Arewa
Wasu daga cikin mazauna Kano sun bayyana fushinsu da damuwa a kan yadda ake ci gaba da kashe Hausawa a jihohi daban-daban ba tare da hukunci ba.
Usman Alasan Tsanyawa, wanda ya zanta da majiyar Legit, ya ce:
“Gaskiyar magana ina kira ga mai girma gwamna da mahukuntan kasar nan su yi kokari su magance wannan matsala ta kashe mana mutane."
"Saboda ba zai yiwu ba a matsayinmu na 'yan Arewa, a ce dan Arewa yana kashe dan Arewa. Ba da dadewa ba an kashe mana mutane a Binuwai, an kashe a Filato, kuma duk Arewa ne.”
Ya cigaba da cewa idan gwamnati ta ci gaba da shiru, matasan Arewa ba za su ci gaba da hakuri ba, kuma hakan na iya haifar da wani babban rikici a gaba.
Martanin gwamnan Kaduna kan kisan Mangu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna bacin ransa kan mummunan kisan gillar da wasu matafiya ‘yan asalin jiharsa suka fuskanta a Filato.
Mutanen da aka kashe na kan hanyarsu ne daga Basawa, Zaria zuwa karamar hukumar Qua’an Pan domin halartar ɗaurin aure, lokacin da suka fada hannun wasu mugayen mutane.
Uba Sani ya kuma bukaci gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, da ya dauki matakan gaggawa domin tunkarar matsalar tsaro da kuma hukunta wadanda suka yi kisan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



