Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban PDP da Ɗansa, Sun Ɗauke Budurwa a Kwara
- Wasu 'yan bindiga sun kashe shugaban PDP na mazabar Lade da dansa da wani mutumi a kauyen Mari da ke jihar Kwara
- Sannan sun sace yarinya 'yar shekara 12 a sansanin Fulani na Aiyetoro da ke kauyen Lile cikin gundumar Patigi
- Rundunar ‘yan sanda da masu gadin gari sun shiga daji domin ceto yarinyar yayin da Bukola Saraki ya yi Allah wadai da kisan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a wani sansanin Fulani da ke jihar Kwara.
Yayin harin, an kashe mutum uku a kauyen Mari tare da sace yarinya ‘yar shekara 12 a sansanin Fulani da ke Lile a Patigi.

Source: Twitter
Yadda yan bindiga suka hallaka shugaban PDP
Jami’an ‘yan sanda a jihar Kwara sun tabbatar da faruwar lamarin da suka ce ya faru da safe a ranar Laraba, 25 ga Yuni, 2025, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka kashe sun hada da shugaban PDP na mazabar Lade, Alhaji Abdullahi Shehu, da dansa Abdullahi Mohammad da wani mai suna Timothy Paul.
A lokaci guda, an sace yarinya mai suna Hassana Abdullahi daga sansanin Fulani na Aiyetoro da ke Lile, cikin mazabar Lade.
Kakakin ‘yan sanda, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya ce:
"Da misalin karfe 1:30 na dare, ‘yan bindiga suka kai hari Mari da Lile, an kashe Timothy Paul (namiji, shekara 35) a Mari, da Alhaji Abdullahi Shehu (namiji, shekara 51) da dansa Abdullahi Muhammad (namiji, shekara 22).
“Likitoci a asibiti sun tabbatar da mutuwar su."

Source: Original
Matakin da yan suka ɗauka a Kwara
A wani lamari daban da misalin karfe 3:00 na safe, ‘yan bindiga huɗu sun shiga sansanin Aiyetoro Fulani suka sace Hassana Abdullahi.
Yarinyar da aka sace ita ce ‘yar Abdullahi Jowuro, an tabbatar da yankin da aka kai harin kuma an gudanar da bincike.

Kara karanta wannan
Yan majalisar Amurka sun ja kunnen Trump bayan ikirarin shirin sulhunta Iran, Isra'ila
‘Yan sanda sun ce an tura jami’ai tare da yan banga da masu farauta don gudanar da bincike da ceto yarinyar.
Sakamakon haka, an fara bincike don gano yan bindiga da ke da hannu a lamarin, kuma za a gurfanar da su idan an kama su.
Ta ce:
“Rundunar tana jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi. Muna kira da a rika bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi.”
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya la’anci kisan shugaban PDP da dansa.
A wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Abdulganiyu Abdulqadir ya wallafa a Facebook, Saraki ya ce harin mugun abu ne, mai ban tausayi kuma ba za a yarda da shi ba.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan su, sannan ya bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa.
Tsohon gwamnan Kwara ya rasu a Abuja
Kun ji cewa jihar ta yi babban rashi bayan rasuwar tsohon gwamna wanda ya bar duniya yana da shekara 84.
Marigayin Cornelius Adebayo wanda ya taɓa yin sanata ya rasu ne da safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Yunin 2025 a Abuja.
Tsohon gwamnan ya kasance ɗan gwagwarmaya a lokacin da yake raye inda yake cikin mutanen da suka riƙa sa'insa da gwamnatin soja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
