'Har Gida Muka Cin Masa': Gwamnatin Zamfara Ta Faɗi Illar da Ta Yi Wa Bello Turji
- Gwamnatin Zamfara ta ce artabun da aka yi da ‘yan bindiga ranar Litinin ya zama wata sabuwar hanya wajen murkushe su gaba ɗaya
- Hadimin gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Manga ya bayyana cewa an kutsa har cikin mafakar dan bindiga inda aka samu gagarumar nasara
- Gwamnatin Dauda Lawal Dare ta ce za ta ci gaba da farautar Bello Turji, yayin da aka ce ya tsere yayin artabun da aka yi da mayaƙansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta yi magana kan yadda take kokarin murkushe dan bindiga, Bello Turji.
Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa faɗan da jami’an tsaro suka gwabza da wani ɗan bindiga ranar Litinin na nuna sabuwar dabarar yaƙi da su.

Source: Facebook
Zamfara: An shammaci Bello Turji a mafakarsa
Mai taimakawa Gwamna kan harkokin tsaro, Alhaji Ahmad Manga, ya ce an kai wannan samame ne da haɗin gwiwar gwamnati jiha da tarayya, cewar rahoton BBC Hausa.

Kara karanta wannan
Rubdugu kan 'yan adawa: An rusa kamfanin kanin Peter Obi bayan cire rawanin Atiku
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manga ya ce tabbas dan bindigar bai yi tsammanin za a cimma sa ba a halin da ake ciki.
Ya ce:
"A gaskiya an same shi a wurin da ba a taba shiga ba, ya gane cewa yanzu ana iya isar masa."
Ya ƙara da cewa an samu nasarori da dama, an kashe mayaƙansa, inda har yanzu ba shi da adadin waɗanda suka mutu a faɗan.
Manga ya ce idan aka ga gawarwaki to na mayaƙansa ne, domin an yi musu illa sosai a wannan artabu da suka shiga.
Ya bayyana cewa tubabben dan bindiga, Bashari Maniya da ya taimaka musu ya mutu ne sakamakon hatsarin mota bayan sun faɗa wani rami yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Har ila yau, ya ce lokacin da aka kai musu ɗauki, an same su ba a hayyacinsu ba, domin motar da suke ciki harbi bai ratsa ta.

Source: Original
Bello Turji: Alƙawarin da gwamnatin Zamfara ta ɗauka
Manga ya ce gwamnatin Zamfara ba za ta fasa farautar Bello Turji ba, za su ci gaba da matsa masa ba dare ba rana.
Ya kara da cewa:
"Wallahi sai abin da ya ci gaba. Kowa a Zamfara ya san irin gallazawar da ya shafe shekaru 14 yana yi wa mutane."
Ya ce Bello Turji ya gane cewa jami’an tsaro sun nuna bajinta, domin an iske shi a gida inda da ba a taɓa samunsa ba.
Gwamnati ta ce za ta kawo ƙarin sojoji domin ci gaba da tinkarar Turji da mayaƙansa a yankin.
Manga ya bayyana cewa a lokacin artabun, Turji yana ta buya kafin daga baya ya arce daga wurin.
An ce Maniya da ɗan’uwansa sun tuba, inda suka shiga taimakon jami’an tsaro, har suka kai hari kan sansanin Turji.
Wasu rahotanni sun ce kafin harin, Turji ya samu bayani, ya tara mayaƙa fiye da dubu domin tinkarar jami’an tsaro.
Turji ya ƙaƙaba haraji a Zamfara
A wani labarin, dan bindiga, Bello Turji ya bukaci N50m daga mazauna Tsallaken Gulbi da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.
Wadanda abin ya shafa sun hada da mutanen kauyen Fakai har zuwa Qaya da ke kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
An tabbatar da cewa Turji ya bukaci kudin ne domin ya bar su su ci gaba da noma a wannan kakar ba tare da sun samu matsala ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

