Gwamnan Kano, Ribadu Sun Halarci Jana'izar Matasa 2 da Aka Yi wa Kisan Gilla a Binuwai

Gwamnan Kano, Ribadu Sun Halarci Jana'izar Matasa 2 da Aka Yi wa Kisan Gilla a Binuwai

  • An gudanar da jana'izar Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja bayan kisan gillar da aka yi masu a Binuwai
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Malam Nuhu Ribadu sun halarci jana'izar, sannan sun raka matasan har makabarta ta Gudu
  • Lamarin na zuwa a lokacin da gwamnatin jihar Kano ke fafutukar tabbatar da adalci a kan kisan mafarautanta 16 a wasu suka yi a jihar Edo

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, sun halarci jana’izar matasa biyu a Abuja.

Wasu mugayen matasa a jihar Binuwai ne suka hallaka matasan biyu ’yan asalin jihar Kano a birnin Makurdi, yayin da suka tsaya shan shayi a hanya.

Kara karanta wannan

Wike ya samu yadda yake so, PDP ta sanar da sahihin sakataren jam'iyya na ƙasa

Gwamnatin Kano ta karbi gawarwarkin matasanta a Abuja
An yi jana'izar matasan Kano a Abuja Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an gudanar da sallar jana’izar ne a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, inda iyalan mamatan da shugabannin addini suka hallara domin jimami da addu’a.

Mamatan, Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, ’yan unguwar Unguwa Uku ne a Kano, kuma an binne su a makabartar Gudu, Abuja, tare da rakiyar Gwamna Yusuf da Nuhu Ribadu.

Gwamnatin Kano ta yi tir da kisan matasan

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Abba, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook, gwamnatin Kano ta bayyana kisan matasan a matsayin abin takaici.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Benue da ta gaggauta cafke da hukunta waɗanda ke da hannu a cikin lamarin.

Jana'izar matasan Kano a Abuja
Gwamnan Kano, Nuhu Ribadu na daga cikin mahalarta jana'izar matasa Hoto: Sanusi D-Tofa
Source: Facebook

A cewar sanarwar:

"Wannan babban rashi ne gare mu a Kano da ma ƙasar nan gaba ɗaya. Ya kamata gwamntin jihar Binuwai ta ɗauki mataki a cikin gaggawa don kama da hukunta masu wannan mugun aiki."

Kara karanta wannan

An kashe yaran Sheikh Ibrahim Khalil a Benue, gwamnan Kano ya yi magana mai zafi

Gwamnan ya jaddada muhimmancin ganin an samu adalci, yana gargaɗin cewa rashin ɗaukar mataki na iya haifar da barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Gwamna ya tunatar da Edo diyyar mafarautan Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma yi amfani da wannan dama don tunatar da Gwamnatin Edo game da buƙatar biyan diyyar mafarautan Kano 16 da suka rasa rayukansu a Uromi.

Mafarautan sun je Edo ne domin dawowa jihar Kano su yi bikin Sallah tare da iyalansu, sai dai wasu miyagun bata-gari suka yi masu kisan gilla a gaban 'yan bijilantin jihar.

Kisan ya haifar da fushi a Arewacin Najeriya, amma manya da shugabanni suka buƙaci a kwantar a hankula tare da kira ga hukuma da ta tabbatar da adalci.

An kashe matasan Kano a Binuwai

A wani labarin, mun wallafa cewa ana zargin wasu bata gari da yi wa matasa biyu ’yan asalin Kano kisan gilla a Makurdi, babban birnin jihar Binuwai ba tare da laifin komai ba.

Matasan da aka kashe su ne Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad, waɗanda suka gamu da ajalinsu yayin da suka tsaya shan shayi da misalin ƙarfe 11.00 na dare.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana bacin ransa kan wannan kisan gillar da ya faru a Makurdi, inda ya bayyana shi da aikin rashin imani da mugunta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng