Gwamna Fintiri Ya Kwace wa Atiku Sarautar Wazirin Adamawa? Ga abin da Muka Sani

Gwamna Fintiri Ya Kwace wa Atiku Sarautar Wazirin Adamawa? Ga abin da Muka Sani

  • An samu rahotanni masu karo da juna kan zargin cire wa Atiku Abubakar sarautar Wazirin Adamawa saboda sabuwar doka
  • Sai dai mai magana da yawun Gwamnan Adamawa ya musanta zargin, yana mai cewa labaran ƙarya ne kawai ake yaɗawa
  • Sabuwar dokar ta tanadi cewa sai 'yan asalin wasu yankuna ne kawai za su iya riƙe irin waɗannan sarautu, abin da ya shafi Atiku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa - An samu rahotanni masu cin karo da juna kan zargin gwamnatin Adamawa ta tube wa Alhaji Atiku Abubakar, sarautarsa ta Wazirin Adamawa.

A rahoton farko, an ce gwamnatin Adamawa ta kawo sabuwar doka da ta buƙaci duk masu riƙe da sarautun gargajiya da 'yan majalisar masarautu su kasance ƴan asalin yankin masarautar da suke.

Kara karanta wannan

Wike ya samu yadda yake so, PDP ta sanar da sahihin sakataren jam'iyya na ƙasa

An samu sabani game da sabuwar dokar Adamawa da ta za ta iya tube rawanin Wazirin Adamawa daga Atiku
Alhaji Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa. Hoto: @atiku
Source: Facebook

An karyata tube rawanin Wazirin Adamawa

Amma, sakataren yaɗa labaran gwamnan Adamawa, Malam Humwashi Wonosikou, ya musanta rahoton, inda ya shaidawa jaridar ThisDay cewa ƙarya ake yaɗawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mrs. Adama Felicity Mamman, babbar sakatariyar ma'aikatar harkokin masarautun Adamawa ta fitar da sanarwa a ranar 20 ga Yunin 2025, wacce ta yi magana kan sabuwar dokar.

Sanarwar ta fayyace batun sabuwar dokar ta da ƙirƙiri sababbin masarautu a jihar Adamawa, wacce Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya gabatar.

A al'adance, Wazirin Adamawa shi ne ke da matsayi na biyu mafi girma a Masarautar Adamawa, bayan Lamido Adamawa.

Yadda sabuwar dokar masarautu ta shafi Atiku

A cewar sanarwar Mrs Adama, sawbuwar dokar da aka yi ta sa ƴan asalin yankunan Yola ta Kudu, Yola ta Arewa, Girei, Mayo-Belwa, Song, da Zumo ne kaɗai za su cancanci rike sarautar Wazirin Adamawa da kuma zama 'yan majalisar Masarautar Adamawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Fintiri ya cire rawanin Atiku, an raba shi da matsayin Wazirin Adamawa

Da wannan sabuwar dokar, an cire Atiku kai tsaye daga sarautar Wazirin Adamawa, domin ya fito ne daga karamar hukumar Jada, wani ɓangare na Masarautar Ganye.

Baya ga Atiku, wannan sabuwar dokar ta shafi wasu masu riƙe da sarautun gargajiya waɗanda ba su cika sababbin buƙatun zama 'yan asalin masarautun da aka yi masu nadin sarauta ba.

Duk da haka, gwamnati ta ci gaba da cewa matakin ya yi daidai da gyare-gyarenta a fannin gudanarwa da ke da alaƙa da sake fasalin masarautun gargajiya.

Gwamnatin Adamawa ta ce ba ta cire rawanin Wazirin Adamawa kan Atiku Abubakar ba
Gwamnan jihar Adamawa, mai girma Ahmadu Umaru Fintiri. Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Zargin rikicin siyasa tsakanin Atiku da Fintiri

Sai dai, lokacin da aka tuntube shi, babban sakataren yaɗa labarai, Wonosikou, ya musanta rahotannin cewa an tube wa Atiku sarautar Wazirin Adamawa.

Mr. Wonosikou ya kuma yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan saɓanin da ake zargin an samu tsakanin Gwamna Fintiri da Atiku Abubakar, inji rahoton Premium Times.

Sai dai, masu sharhi kan harkokin siyasa sun danganta lokacin da aka fitar da wannan sabuwar dokar da rikicin da ake zargin yana ƙaruwa tsakanin Fintiri da Atiku.

An nemi Atiku ya hakura da takara a 2027

Kara karanta wannan

2027: Barau ya yi magana bayan an nemi Tinubu ya ajiye Shettima ya dauke shi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara, ya bukaci Atiku Abubakar da ya dakatar da neman shugabancin Najeriya.

A cewar Baba-Ahmed, ya kamata Atiku ya rungumi rawar uban al'umma domin ci gaban ƙasar domin ya cancanci zama gwarzon dimokuraɗiyya.

Ya kuma buƙaci Atiku da ya mai da hankali kan samar da sabbin shugabanni matasa, waɗanda za su iya jagorantar Najeriya a madadin APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com