Adamawa: Za a nada Adamu Atiku Abubakar a matsayin sabon Sardaunan Ganye

Adamawa: Za a nada Adamu Atiku Abubakar a matsayin sabon Sardaunan Ganye

Mun samu labari cewa za a nada Alhaji Adamu Atiku Abubakar a matsayin sabon Sardaunan Ganye, a Kudancin jihar Adamawa.

Kafin yanzu tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ne ya ke rike da wannan sarauta ta Sardaunan kasar Ganye.

Atiku Abubakar mai shekaru 73 a Duniya ya sallama rawaninsa ga daya daga cikin ‘ya ‘yan cikinsa domin ya yi gadon wannan sarauta mai girma.

Mustapha Atiku Abubakar shi ne ya fara bayyana wannan sauyi da aka samu a masarautar Ganye. Mustapha ya taya ‘danuwansa murna ne a shafin Twitter.

“Ina taya yaya na Adamu Atiku Abubakar murna na nada shi da aka yi a matsayin sabon Sardaunan Ganye.” Inji Mustapha Atiku Abubakar a safiyar Litinin.

KU KARANTA: 2023: Atiku Abubakar zai sake neman takarar Shugaban kasa

Adamawa: Za a nada Adamu Atiku Abubakar a matsayin sabon Sardaunan Ganye
Adamu Atiku Hoto: Facebook
Asali: Twitter

Mustapha ya ke cewa Adamu ya cancanci wannan nadi, sannan ya ce: “Godiya ga Mahaifinmu, Wazirin Adamawa Atiku Abubakar da ya cire wannan rawani, ya mikawa ‘danuwanmu.”

Sabon Sardaunan ya ji dadin wannan sakon taya murna na ‘danuwansa, ya kuma yi masa godiya.

Wazirin Adamawa, Atiku ya yi wa magajin na sa addu’a, ya ce ya na fatan wannan nadi ya zama silar budewar alherori a kofarsa.

Kwanakin baya Atiku Abubakar ya yi irin haka, inda ya bar wa ‘dansa Aliyu Atiku sarautar Turakin Adamawa bayan ya zama sabon Wazirin kasar Adamawa.

A halin yanzu Adamu Atiku shi ne kwamishinan ayyuka na jihar Adamawa, ya kuma yi aiki da kamfanin INTELS Nigeria na mahaifinsa a baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel