Rubdugu kan 'Yan Adawa: An Rusa Kamfanin Kanin Peter Obi bayan Cire Rawanin Atiku
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya bayyana damuwa kan yadda ake take hakkin dan Adam a Najeriya
- Peter Obi ya ce an rusa ginin kamfanin ɗan uwansa a Ikeja, Lagos, ba tare da wata doka ko takardar kotu ba
- Obi ya ce irin wannan rashin bin doka da oda na karya ƙasa tare da kuma hana masu zuba jari amincewa da Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lagos - Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana yadda aka yi rusau a kamfanin ɗan uwansa.
Peter Obi ya ce an ruguza kamfanin dan uwansa a Ikeja, jihar Lagos, ba tare da bin wata hanya ta doka ba.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a X, Obi ya bayyana lamarin a matsayin “babban abin takaici” wanda ya nuna yadda doka ke ci gaba da dusashewa a ƙasar.
Obi ya ce irin wannan abu da ya faru da shi kai tsaye yana ba shi damar fahimtar irin azabar da talakawa da ƙananan ‘yan kasuwa ke fuskanta kullum sakamakon rashin doka da adalci.
Peter Obi ya yi zargin rashin bin doka
Obi bayyana takaicinsa cewa har yanzu babu wanda ya bayyana da cikakken bayani kan wanda ya bayar da umarnin rushe ginin.
A cewarsa:
“Ina cikin taro ne a Abuja lokacin da ƙanina ya kira cikin gaggawa cewa an shigo da wasu mutane da injin rushe gida zuwa kamfanin da ke Ikeja, suka fara rushe masa gini.”
Vanguard ta wallafa cewa Obi ya ce ya gaggauta komawa Lagos, inda ya bukaci ganin takardar umarnin kotu da ta ba su su izinin rusau din.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda Shugaba Tinubu ya gabatar da abokin karatunsa a Amurka ya ƙayatar da jama'a
Sai dai abin mamaki, a cewarsa, sun nuna masa hukuncin kotu ne da aka yanke wa wani “mutum marar suna” wanda babu wanda ya san ko waye.
Ya yi tambaya da cewa:
“Ta yaya kotu za ta yanke hukunci kan wanda ba a san ko waye ba?”
Wanene ya rusa kamfanin kanin Peter Obi?
Peter Obi ya ce babu wata takardar rushe gini daga gwamnati, kuma babu wanda ke iya bayyana wanda ya bayar da umarnin.
Ya ce:
“Wanda ke da injin rushe-rushen ya ce bai san wanda ya turo shi ba.
"Daga karshe sai wasu mutum biyu suka zo suka ce mu tafi ofishin ‘yan sanda, amma su ma ba su da takardar wani umarni daga kotu,”
Obi ya ce wannan al’amari yana daga cikin abubuwan da ke sa masu zuba jari tsoron zuwa Najeriya.

Source: Facebook
Ya kawo misalin wani dan kasuwa da ya ce ya zuba jari a Ghana da Senegal, amma ba zai taba saka kudinsa a Najeriya ba saboda rashin doka.
Peter Obi ya fitar da bayanin ne jim kadan bayan fitowar bayanai kan cire rawanin Atiku Abubakar a matsayin wazirin Adamawa.
Obi ya bukaci Tinubu ya ziyarci jihohi
A wani rahoton, kun ji cewa Peter Obi ya yaba da kokarin da shugaba Bola Tinubu na zuwa jaje jihar Benue.
Sai dai duk da haka, Obi ya ce zama bai kama Bola Tinubu ba lura da akwai sauran jihohi da ya kamata ya ziyarta.
Peter Obi ya ce ya kamata Bola Tinubu ya yi koyi da shugabannin duniya wajen tausaya wa mutanen da suka shiga bala'i.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

