Ndume Ya Fadi Yadda Mulkin APC Ya Damalmale saboda Makusantan Tinubu
- Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya cika gwamnati da mutanen da ba za su iya fada masa gaskiya yadda ya kamata ba
- 'Dan majalisar ya bayyana cewa wannan na daga cikin abubuwan da za su iya jawo matsala ga tafiyar da gwamnati kuma barazana ce ga kasa
- Ndume ya soki yadda aka yi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai cewa bai cancanci yadda aka yi masa a gwamnatin Tinubu ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kewaye kansa da mutane masu iya faɗa masa gaskiya.
Sanata Ali Ndume ya yi zargin cewa a yanzu haka, Shugaban Najeriyan na kewaye ne da mutanen da ba za iya shaida masa gaskiyar da ya kamata ya ji.

Source: Facebook
Arise News ta wallafa cewa Ndume ya ce Tinubu wanda ya kasance uba siyasa a baya, kuma ya cika gwamnatin sa da 'yan amshin shata da ba za su iya kallon idonsa su faɗi gaskiya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada cewa wannan hali na rashin gaskiya a kusa da shugaban ƙasa, yana iya janyo illa ga kasa, domin kuwa babu wanda ke iya faɗa masa gaskiya.
Ndume ya soki yadda aka matsawa El-Rufa’i
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Sanata Ndume ya ce tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, bai cancanci yadda aka yi masa a gwamnatin Bola Tinubu ba.
Ya ce:
"Ba a kafa gwamnati da masu dogaro da kai. Abu mafi muni shi ne, shugaban ƙasa ya kasance jagora a siyasa. Amma idan mai jagora ya zama sarki, to sai ya gane cewa akwai matsala."
Ndume ya yi magana kan rushewar APC
A lokacin hirar, Ndume, wanda ya jagoranci yaƙin neman zaɓen Rotimi Amaechi a zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa na 2023, ya ce jam’iyyar APC na iya rushewa.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa bayan Tinubu ya zama ɗan takara, Amaechi ya amince ya yi aiki tare da shi. Sai dai duk da an tsara ganawa tsakanin bangaren Tinubu da na Amaechi, hakan bai samu ba.
Ya tabbatar da cewa akwai alamun za a samu matsala babba matukar babu wadanda za su iya shaida wa Bola Tinubu abubuwan da ya dace ya saurara.
'Zan iya fice wa daga APC,' Sanata Ndume
A baya, mun wallafa cewa Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya fice daga jam’iyyar APC idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaza gyara al’amuran ƙasar nan.
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya ce yana sa ido kan yadda gwamnatin Tinubu ke tafiya, inda ya jaddada cewa burinsa tun farko shi ne ganin Tinubu ya yi nasara a shugabancin ƙasar.
Ndume ya bayyana cewa ya halarci wasu daga cikin tarurrukan da shugabannin jam’iyyun adawa ke gudanarwa da nufin kafa haɗaka domin kalubalantar Tinubu a zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

