Wata Sabuwa: Rikici Ya Barke a SDP bayan Dakatar da Shugaban Jam'iyya
- Ƴan daba sun kai farmaki a hedkwatar jam'iyyar SDP ta ƙasa da ke Abuja a ranar Talata, 24 ga watan Yunin 2025
- Lamarin ya auku ne biyo bayan dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa da wasu manyan jagorori a majalisar NWC
- Ƴan jaridan da suke a hedkwatar jam'iyyar a birnin tarayya sun ji a jikinsu biyo bayan ritsa su da ƴan daban suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An samu tashin hankali bayan ƴan daba cikin baƙaƙen kaya sun farmaki hedkwatar jam'iyyar SDP da ke Abuja.
Ƴan daban waɗanda suka kai hari a hedkwatar sun farmaki ƴan jarida da ma’aikatan jam’iyyar a ranar Talata.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce harin ya faru ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara tsananta cikin SDP, sakamakon dakatar da wasu manyan jami’an jam’iyyar na ƙasa.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Jami'an DSS sun cafke rikakkun 'yan bindiga bayan dawowa daga Saudiyya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar SDP ta dakatar da manyan NWC
Daga cikin manyan shugabannin jam'iyyar da aka dakatar har da shugaban SDP na ƙasa, Alhaji Shehu Gabam.
Kwamitin gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar ya sanar da dakatar da Shehu Gabam, mai binciken kuɗi na ƙasa, Nnadi Clarkson, da shugaban matasa na ƙasa, Chukwuma Uchechukwu.
Ana zargin su da aikata munanan laifuffuka na almundahana da suka haɗa da wawurar kuɗi, karkatar da su ba bisa ƙa’ida ba da kuma amfani da su ta hanyoyin da ba su samu amincewar jam’iyya ba, waɗanda suka kai ɗaruruwan miliyoyin Naira.
Ƴan daba sun kai farmaki a ofishin SDP
Ƴan jarida da suka hallara a ofishin jam’iyyar domin wata ganawa da manema labarai sun tsinci kansu cikin rikici yayin da ƴan daban suka afka musu.
An kwace kyamarori da wayoyin hannu, sannan wasu ƴan jarida an yi musu dukan tsiya kafin jami’an tsaro suka kawo ɗauki wajen daƙile lamarin.

Kara karanta wannan
ADA: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabuwar jam'iyyarsu Atiku da El Rufai
Harin ya zama a bainar jama’a ne bayan da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Rufus Aiyenigba, ya fitar da wata sanarwa yana bayyana dakatarwar.

Source: Facebook
Meyasa aka dakatar da shugaban SDP?
"Wannan hukuncin ya biyo bayan kudurorin da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa suka cimma, inda aka gabatar da kwararan hujjoji da suka nuna yadda jami’an da aka dakatar suka shiga mu’amaloli da kuɗin jam’iyya ba tare da izini ba."
"Suna amfana da su ta hanyoyin kai-da-kai da kuma cirewa daga asusun jam’iyya ba tare da amincewar kwamitin ba."
- Rufus Aiyenigba
A cewar shugabannin jam’iyyar, lamarin ya ƙara tsananta ne bayan Gabam ya gabatar da bayanan kuɗi ga hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ba tare da amincewar jam’iyya ba, sannan ya sanya rahoton a cikin kafafen yaɗa labarai.
Jam'iyyar SDP ta yi sababbin nade-nade
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar SDP ta yi sababbin nade-nade a kwamitin gudanarwarta na ƙasa (NWC).
Jam'iyyar ta yi naɗin muƙamai ciki har da na mataimakan shugaban jam'iyya a yankunan Kudu da Arewacin Najeriya.
Daga cikin waɗanda SDP ta naɗa akwai Sanata Ugochukwu Uba a matsayin mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa (Kudu) da Farfesa Sadiq Umar Abubakar a matsayin mataimakin shugaban jam’iyya (Arewa).
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng