Jami'o'in Najeriya 3 Sun Shiga Jerin Manyan Makarantun Duniya

Jami'o'in Najeriya 3 Sun Shiga Jerin Manyan Makarantun Duniya

  • Jami’ar Ibadan, Jami’ar Legas da Jami’ar Ahmadu Bello ne kaɗai a Najeriya suka samu shiga cikin jerin jami’o’i masu nagarta na duniya
  • Rahotanni sun nuna cewa jami’o’in UI da UNILAG sun kasance a mataki na 1001- 1200, yayin da ABU ke a matsayi na sahun 1201–1400
  • Bincike ya nuna cewa Najeriya na baya a nahiyar Afrika idan aka kwatanta da kasashe irin su Masar, Afirka ta Kudu da Tunisia

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Cibiyar nazari ta QS ta fitar da jerin jami’o’in da suka fi nagarta a duniya na shekarar 2026.

Bayanin da cibiyar ta fitar a makon da ya wuce ya nuna cewa jami’o’i uku ne kawai daga Najeriya suka samu shiga.

Jami'ar ABU da wasu makarantun Najeriya sun shiga jerin jami'o'in duniya.
Jami'ar ABU da wasu makarantun Najeriya sun shiga jerin jami'o'in duniya. Hoto: Ahmadu Bello University Zaria
Source: Twitter

Rahoton Vanguard ya nuna cewa wadanda suka samu shiga jerin sun hada da Jami’ar Ibadan (UI), Jami’ar Legas (UNILAG) da kuma Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU).

Kara karanta wannan

2027: Masu hadakar kafa ADA sun samu kalubalen farko daga ministan Tinubu

UI da UNILAG sun kasance a matsayin 1001 zuwa 1200, wato dai matakin da suka samu a shekarar 2025. ABU ta bayyana a karo na farko a matsayin 1201 zuwa 1400.

Me aka yi la’akari da shi a tantance jami’o’in?

Cibiyar QS ta bayyana cewa ta yi la’akari da fannoni daban-daban wajen fitar da jerin, ciki har da martabar jami’ar a idon malamai da masu daukar ma’aikata.

Ta kara da cewa ta lura da yawan dalibai idan aka kwatanta da adadin malaman da suke koyar da su, yawan binciken kimiyya, yawan daliban ƙasashen waje da ke karatu a jami’ar.

Legit ta rahoto cewa QS ta yi lura da haɗin gwiwar bincike da sauran jami’o’i a duniya, damar samun aiki bayan kammala karatu da kuma ingantacciyar manufofin dorewar cigaba.

A cikin jami’o’i 297 da hukumar NUC ta amince da su a Najeriya, uku ne kacal suka samu shiga wannan jerin. A duniya kuwa, jami’o’i 1,501 ne daga ƙasashe 106 suka shiga jerin a 2026.

Kara karanta wannan

Malaman addini sun ayyana ranar azumi da addu'oi domin zaman lafiya a Najeriya

Najeriya na baya a jerin jami’o’in Afrika

A matakin nahiyar Afrika, Najeriya na baya-baya idan aka kwatanta da wasu jami'o'in ƙasashen yankin.

Masar ta fi kowace ƙasa da jami’o’i 20 a cikin jerin, sai Afirka ta Kudu da ke da 11, Tunisia da jami’o’i 4, sannan Ghana da Morocco da ke da jami’o’i biyu-biyu.

Kasashen Kenya, Libya, Sudan, Uganda da Habasha sun samu wakilci da jami’a guda-guda kowannensu.

Wannan na nuna irin gibin da ke akwai tsakanin Najeriya da sauran ƙasashen nahiyar a fannin ilimi mai zurfi.

Jami’o’i mafiya daraja daga Afrika su ne jami'ar Cape Town da ke Afirka ta Kudu wanda ta samu matsayi na 150, da kuma jami'ar Witwatersrand da ke matsayi na 291 a duniya.

Jami'ar Legas ta shiga jerin manyan jami'o'in duniya
Jami'ar Legas ta shiga jerin manyan jami'o'in duniya. Hoto: University of Lagos
Source: UGC

Malamin jami'ar Jigawa ya kafa tarihi a duniya

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin jami'ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa ya kafa tarihi a duniya.

Malamin jami'ar mai suna Dr Zaidu Jibril ya samu kyautar gasar fassara ta duniya da kasar Saudiyya ke yi.

Binciken Legit Hausa ya gano cewa Zaidu Jibril ne dan Afrika na farko da ya lashe kyautar saboda muhimman ayyukan da ya yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng