Amurka Ta Risina, Ta Roki China Ta Shawo kan Iran a kan Rufe Hanyar Hormuz

Amurka Ta Risina, Ta Roki China Ta Shawo kan Iran a kan Rufe Hanyar Hormuz

  • Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya roki China da ta ja kunnen Iran kada ta rufe hanyar Hormuz
  • Rubio ya ce matakin rufe mashigin zai iya haddasa rikicin tattalin arziki da kuma kara rikitar da yankin Gabas ta Tsakiya
  • Hakan na zuwa ne bayan Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran da jiragen sama da makamai masu linzami

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Amurka ta bukaci gwamnatin China da ta shawo kan Iran dangane da yunkurin da Tehran ke yi na rufe hanyar Hormuz.

hanyar Hormuz dai wata muhimmiyar mashiga ce da kashi 20 na mai da iskar gas na duniya ke wucewa ta cikinsa.

Amurka ta roki China ta hana Iran rufe hanyar Hormouz
Amurka ta roki China ta hana Iran rufe hanyar Hormouz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Reuters ya nuna cewa sakataren harkokin wajen Amurka kuma mai ba da shawara kan tsaro na kasa, Marco Rubio, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Abin da ya faru a Qatar bayan Iran ta harba makami mai linzami kan sojojin Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran Amurka ga China kan Hormuz

Kiran na zuwa ne bayan rahotannin da ke cewa majalisar dokokin Iran ta amince da kudurin rufe hanyar a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ta kai kan wuraren nukiliyar ta.

Rubio ya ce:

“Ina rokon gwamnatin China da ke Beijing da ta kira Iran domin dakatar da wannan yunkuri, domin China na da bukata a hanyar wajen samun man fetur daga Gabas ta Tsakiya.”

CNB ta rahoto ya ƙara da cewa:

“Idan suka rufe hanyar, hakan zai zama babban kuskure.
"Wannan zai zama kamun kai na tattalin arziki ga Iran da kuma illa ga sauran ƙasashe fiye da yadda zai shafi Amurka. Ya kamata sauran ƙasashe su kula da hakan.”

Rubio ya bayyana cewa duk wani yunkuri na rufe hanyar zai zama karin rikici da kuma yunkurin da zai bukaci martani daga Amurka da sauran ƙasashe da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Yakin Israila: Abin da ya sa Amurka ta ke tsoron Iran a duniya Inji Bulama Bukarti

Me ya fara hada Iran da Amurka?

Rahotanni daga jami’an gwamnatin Amurka sun ce sojojin Amurka sun lalata manyan cibiyoyin nukiliyar Iran ta hanyar amfani da bama-bamai.

Amurka ta yi amfani da makamai masu linzami nau’in Tomahawk sama da guda 24 da kuma jiragen yaki sama da 125 wajen kai harin.

Wannan mataki ya nuna yadda rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da tsananta, musamman bayan ci gaba da adawar diflomasiyya tsakanin Washington da Tehran.

Hoton ruwan Hormuz da ya ratsa ta Iran
Hoton ruwan Hormuz da ya ratsa ta Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ba a samu martanin China ba har yanzu

A yayin da ake ganin cewa China na iya taka rawa wajen hana Iran ɗaukar matakin rufe mashigin, har yanzu ofishin jakadancin China da ke Washington bai fitar da wata sanarwa ba.

Mashigin Hormuz na daya daga cikin mahimman hanyoyin kasuwancin mai a duniya, kuma duk wani rikici da ya shafi wannan wuri na iya jefa kasuwannin man fetur cikin rudani.

Dangantakar Iran da Amurka

Dangantaka tsakanin Amurka da Iran ta dade da tsamia gabar siyasa tun bayan juyin juya halin 1979 a Iran, wanda ya kifar da gwamnatin Shah da Amurka ke marawa baya.

Kara karanta wannan

Kaikayi koma kan mashekiya: Yadda kai hari a Iran zai shafi tattalin Amurka

Bayan juyin, gwamnatin addinin Islama ta Ayatollah Ruhollah Khomeini ta hau mulki, kuma aka kwace ofishin jakadancin Amurka a Tehran tare da tsare ma’aikatansa na tsawon kwanaki 444.

Wannan lamari ne ya hargitsa huldar diflomasiyya tsakaninsu har zuwa yau, wanda da yawa a duniya ba a sani ba.

Menene ya biyo baya raba garin Iran da Amurka?

Daga nan, Amurka ta sanya takunkumi na tattalin arziki kan Iran, musamman dangane da shirin nukiliyarta.

Iran na zargin Amurka da son kawo cikas ga ci gabanta, yayin da Amurka ke ganin Iran barazana ce ga tsaron duniya.

A shekarar 2015 an kulla yarjejeniyar nukiliya (JCPOA) tsakanin Iran da manyan ƙasashe, ciki har da Amurka, amma Donald Trump ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar a 2018, lamarin da ya kara dagula alakar.

Tun daga lokacin, akwai karancin amincewa da juna, hare-hare, da barazanar rufe hanyar Hormuz wacce ta kasance muhimmiyar mashiga da ke da tasiri ga tattalin arzikin duniya.

Rikici tsakanin su na ci gaba da barazana ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kasuwannin duniya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

'Kun shiga uku': Iran ta faɗi abin da za ta yi wa Amurka bayan hari a cibiyoyin nukiliyarta

'Yan Najeriya sun makale a Iran da Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Najeriya da dama sun makale a kasashen Iran da Isra'ila yayin da ake cigaba da gwabza fada.

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa suna cikin tashin hankali kuma suna bukatar taimakon gaggawa daga gida.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana kan kokarin ganin ta ceto mutanenta da suka makale a kasashen cikin aminci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng